Makalu

Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

 • Alfanun tsiro ko ganye a matsayin abinci ko hanya ta samar da waraka (magani) daga wasu nau’o’in cututtuka ga ɗan Adam daɗɗaɗe abu ne a tarihi. Don haka, kusan kowace al’umma ta tanadar da hanyoyin sarrafa nau’ukan abincinta da kuma samar da kariya ko magungunan gargajiya don jinyar cututtukan jiki daga tsirrai da wasu ganyayyaki da suke samu a yankunansu. Kuma babu mahaluki da zai bugi ƙirji ya ce ya san haƙiƙanin a ina ko lokaci da aka fara amfani da ganye (tsiro) a matsayin hanyar jinyar cututtuka, sai dai kuma dangantaka tsakanin tsirran da lafiya ya wanzu ne tun farkon samuwar ɗan Adam a doron ƙasa.

  Hujja ta kusa da ke bayyana dangantaka ta ƙut-da-ƙut tsakanin waɗannan an same su ne cikin wasu ƙungiyoyin addini da kuma wasu muhimman takardun da suka shafi kayakin kimiyya a cikin kabarin Neanderthal man (wanda ake danganta shi da samuwar ɗan adam) da ke binne tun shekaru dubu sittin (60,000) da suka gabata.

  Wani binciken ƙididdiga kuma ya bayyana cewa wasu daga cikin nau’ukan tsirrai da aka binne da gawar a cikin kabarin duk suna taimakawa wajen magani. Sannan kuma kiciɓis da aka yi wajen binciko sabon tsiro na abinci ko a matse ruwansa wanda yake taimakawa wajen rage raɗaɗi da zafin ciwo musamman ma zazzaɓi, na iya samun nasaba da kasantuwar wannan ilmin wanda ya shuɗe sanna ya yi naso cikin zuri’ar al’umma, wanda daga ƙarshe ya zama silar samuwar magani.

  Kuna iya karanta: Yadda za a rage sugar a cikin jini ba tare da shan magani ba

  Haka kuma a wata ƙididdiga wadda ta nuna cewa yawan mutane da ke zaune cikin karkara kashi 75% zuwa 90% a duniya har gobe sun dogara ne da magungunan da waɗannan tsirrai ke samarwa a matsayin babbar hanyarsu ta kiwon lafiya. Wannan hanyar kuwa ta maganin gargajiya ta cigaba da bunƙasa a ƙasar sin (China) a yau da ƙasar India da ma wasu ƙasashe na duniya wanda har da Najeriya.

  Ganyen Bi-ni-da-zuga

  Ita wannan bishiya ta Bi-ni-da-zuga ana kiranta da sunaye daban-daban a sassan duniyan nan dangane da yadda al’umma suka santa da shi bisa tsarin al’adarsu. A wasu wuraren ko ƙasashe ana kiranta, pignut, ko purge nut, ko Barbados nut, ko kuma Black vomit nut. A ƙasashen Asiya kuma musamman ma ƙasar India, a yawa-yawan lokaci ana ƙiran bishiyar da ‘Castor oil plant’ ko kuma ‘hedge Castor oil plant’   A Najeriya kuma, al’ummar Hausawa na ƙiranta Bi-ni-da-Zuga, ƙabilar Igbo kuma suna kiranta da Olulu idu ko Owulu idu. ƙabilar Yoruba kuma suna kiranta Botuje, ko lapa lapa fun fun. Ya yin da ƙabilar Fulani kuma ke kiranta da kwalkwalaje a harshensu na Fillanci.

  Tsarin Bi-ni-da-Zuga (Jatropha Curcas)

  Bi-ni-da-zuga, shi dai bishiya ne wanda dangane da tsarinsa, yayin da ya girma matuƙa, yana kai kimanin mita 3-4 ko kuma 3 zuwa 8 na tsawo. Daga cikin zuri’arsa akwai ire-irensa kusan kimanin ɗari biyu da tamanin da uku (283) da wasu nau’ukan tsirrai ko shuka da suka kai kimanin dubu bakwai da ɗari uku, waɗanda suke iri guda a duk faɗin duniyar nan a mabambantan yankuna waɗanda yanayinsu ya bambanta. Shi dai Bi-ni-da-Zuga, dangane da yanayi,  buƙatar fari (rashin ruwa) amma kuma an iya shuka shi ko yana iya tsira a sahara ko rairayi, sannan yana iya tsira ko fita a ko ina yake kuma a kowane iri nau’i na ƙasan shuka, ko a taɓo ko yashi ko a inda duwatsu suke don bai damu da ko akwai fari ba (rashin ruwa) sannan yana iya rayuwa kusan shekaru hamsin (50), sannan kuma babu wani ƙwaro dake addabarsa balle ya masa illa.

  Bishiyar Bi-ni-da-zuga na da gajerun gaɓa na jikinsa sannan yana da rassa daga jikin kowane gaɓa na shi. Sannan bishiya ne da jikinsa ke da laushin gaske kuma fatar jikin bishiyar na nan kore-kore da wani ɗan layi fari-fari a jiki. Dangane da tsarin ganyensa kuma, ganye ne falafala ba su da tsayi sai faɗi wanda faɗin ya kai kimanin 2 - 6 mm. Sannan ganyen kan canja launinsa a wasu lokuta zuwa wani launi na rawaya, sannan kuma furen bishiyar Bi-ni-da-zuga yana da launi kore-kore da rawaya wanda faɗi da tsayin furen ya kai 6 – 7 cm sannan yana da ganye guda biyar a jikin furen.

  Karanta makala makamancin wannan: Amfani 10 na kayan kamshi (spices) ga lafiyar bil adam

  Haka kuma bishiyar na samar da 'ya'ya daga jikinsa wanda lokacin da suke ƙanana  suna da launi kore-kore idan kuma sun girma sun ƙosa sai su sauya daga launin kore zuwa fatsi-fatsi, ko launin ƙasa. Daga cikin kowane kwanso na abin da bishiyar ke samarwa ana samun iri guda uku (seed) na 'ya'yan jikin shi. 'ya'yan tsiron suna nan matsakaita wanda sun kai 3.5cm. Dangane da yanayin tashi, bishiya ne mai saurin girma cikin ƙalilan lokaci zai bunƙasa. Yana kafuwa a ƙasa a cikin wata ɗaya kacal bayan an dasa shi, daga nan ya cigaba da bunƙasa har tsawon shekaru arba’in.

  Yanayinsa

  Dangane da yanayi, Bi-ni-da-zuga ana iya samunsa a layin da yake a latitude na 23026. Sannan yana buƙatar zafi ko dayake yana iya jure zuban dusan ƙanƙara a matsakaicin yanayi. Bi-ni-da-zuga na daga cikin zuri’ar  pantropical duk da yake yana da alaƙa  da guri mai mai yanayin zafi da ruwa, amma yana bunƙasa a kowane ɓangare na ƙasashen Afirka da na Asia

  Wasu alfanun Bi-ni-da-zuga

  Itacen da kuma 'ya'yan itatuwan Bi-ni-da-zuga za a iya amfani da su a wurare daban-daban a ɓangarori da dama har ma a matsayin makamashin wuta.

  1. Da farko, ɗan itacen na ɗauke da wani mai da ake kira viscous oil wanda nauyinsa ya kai (0.50%) wanda ake sarrafa su wajen samar da candles da kuma sabulu a ma’aikatar da suke samar da sarrafa kayan kwalliya na shafawa a fuska ko a jiki.
  2. Ana yin amfani da itacen wajen dafa abinci ko a yi amfani da shi domin ya haskaka wuri a matsayin diesel ko paraffin (wani mai ne da ake samu daga cikin man fetur).
  3. Bi-ni-da-zuga na taimaka wa sinadarin organic (wanda ya shafi abin da abubuwa masu rai suka samar a ƙasa) kamar tana (earth-worm) wanda yake ƙara inganta darajar ƙasa (soil).
  4. Bi-ni-da-zuga in ya tsira a wuri yana taimakawa wajen magance matsalar zaizayan ƙasa (soil erosion) da gusar da tarin ƙasa, daga fari (drought)
  5. Ana kuma amfani da itacen Bi-ni-da-zuga wajen iyakance yanki (boundary fence)
  6. Ana kuma amfani da 'ya'yan itacen Bi-ni-da-zuga a matsayin maganin ƙwari, kamar farin ɗango da kuma gara, sannan ganyen na warkar da murar dabbobi, sannan kuma furannin itacen abin sha’awa ce ga ƙudar zuma. Sannan kuma ɓawon itacen ana amfani da shi wajen samun sinadarin sauya launin tufa kamar blue dye, gray dye, purple dye
  7. Biyo bayan abin da aka ambata a baya da suka jiɓanci alfanun Bi-ni-da-zuga ya sanya al’ummar karkara zantawa domin binciko wa kan su makamashi da zai maye gurbin wanda suke amfani da shi wato fossils fuels (tsiro da ta rayu shekaru masu yawa da suka wuce, wacce aka kiyaye ta ajikin dutse)

  To waɗannan da ma wasu da ba alissafa ba na daga cikin alfanun da ake samu daga itacen Bi-ni-da-zuga.

  Mai karatu na iya duba: Abubuwan da ya kamata a sani game da ciwon hawan jini

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All