Makalu

Amfanin man zaitun guda 5 ga lafiyar jikin ɗan Adam

 • Al'umma da dama ne suka jima suna amfani da man zaitun a ƙasashe ko yankunan da suke kewaye da kogin Mediterranean, a abinci  da kuma wasu cututtuka da ke addabar jikinsu.

  Bincike da ake gudanarwa yanzu ya taimaka wajen bankaɗo wasu daga cikin ababe masu muhimmanci da ke ƙunshe cikin man zaitun ɗin waɗanda suka sanya ya zamo mai amfani ga lafiyarmu. Bayan amfani da man ke yi a abinci a gidaje daban-daban, to rashin samun wasu ababe cikinsa kamar: gluten, da trans fat da kuma cholesterol ya sanya shi ya zama abin dogaro wajen magance wasu cututtuka da suke addabar lafiyarmu. Dangane da haka ne muka yi ƙoƙari wajen tantancewa da zaƙulo wasu muhimmai daga cikin amfanin man zaitun ɗin guda biyar (5) kamar yadda za ku gani a kasa.

  1. Kariya daga kamuwa da cutar daji (cancer).

  Cutar daji (Cancer) na ɗaya daga cikin manyan cututtuka da suka watsu suke yi wa al’umma illa, a faɗin duniyar nan. Kamar yadda binciken wata ƙungiyar masana kimiyya na Turawan Spaniya Spains ya nuna a kan man zaitun, masanan sun nuna cewa, man ɗin na ɗauke da wani sinadari da ake kira ‘antioxidants’ wanda yake rage ko kawar da abin da ke kawo cutar daji, wanda zai sa jiki ya sakata.

  Haka kuma man zaitun na ɗauke da sinadarin oleic acid wanda ke taimakawa wajen rage ƙiba ko ƙona kitse a jiki, kana ya yaƙi watsuwar tumours wanda ke haifar da cutar Nono (breast cancer).

  Kuna iya karanta wannan makala ma: Takaitaccen bayani game da amfanin man zaitun

  An kuma yi amanna da wasu sinadaran da ke cikin antioxidants a man zaitun waɗanda suke taimakawa wajen watsuwar malignant melanoma a fatar jikin ɗan Adam. Sannan man zaitun na iya taimakawa wajen kare sake kamuwar waɗanda suka taɓa jinyar cutar daji (former cancer patients). Haka kuma man zaitun na ɗauke da sinadarin lignan da squalene waɗanda su ma suna taimakawa wajen kare jiki daga kamuwa da cutar daji (cancer).

  2. Yana taimakawa wajen magance ciwon suga (diabetes)

  Man zaitun na magance ciwon suga, kamar yadda bincike da aka wallafa ya nuna a wata mujalla ta cibiyar kula da cutar hawan jini (Diabetes Care Journal) man zaitun na taimaka wa al’umma da suke kewaye da Mediterranean, a irin nau’in abincin da suke ci wajen kare su daga hanyar kamuwa da nau’in cutar daji na biyu (type 2 diabetes) da kashi hamsi (50%). A lokacin da aka yi amfani da cokali 2 kacal na man zaitun ɗin, sannan ya sanya kuzari ga sinadarin da ke rage yawan sikari a jiki (insulin).

  Domin samun ingantaccen lafiya, masana ƙwararru a fannin yaƙi da cutar suga sun ƙarfafa a ci abinci da ke taimaka wa jiki daga 'ya'yan itatuwa kamar, soluble fibre, vegetables, da kuma man zaitun wanda ke ɗauke da sinadarin da ke taimakawa wajen rage ƙiba ko ƙona kitse a jiki mono-saturated fats. Haka kuma, ga waɗanda suka karanta wannan makala za su fahinci yadda al’umma da suke kewaye da Mediterranean, suka fa’idantu da man zaitun wajen inganta lafiyar jikinsu.

  3. Man zaitun na taimakawa wajen ƙona kitse a jiki

  Man zaitun shi kansa wani sinadari ne a abinci wanda yake taimakawa wajen inganta abin da ke ƙona kitse a jiki, da kuma jin rashin sha’awar cin abinci. To amma amfani da man zaitun ɗin na sanya sha’awar cin abinci. Haka kuma man zaitun na taimakawa wajen narkar da abinci, sannan yana taimakawa wajen rike abin da aka ci don rage yawan ciye-ciyen abin da za su sa ƙiba sannan ya daidaita nauyin mutum.

  A wani bincike da masana kimiyya a Spaniya (Spanish scientists) suka gudanar a Jami’ar Navarra da Las Palmas de Gran Canaria na ƙasar na Spain sun gano cewa, man zaitun na taimakawa wajen kiyaye kamuwa da cutar taɓin hankali da ke shafar ƙwaƙwalwa kamar wadda baƙin ciki ke haifarwa, tare da ƙone kitse, domin kitse ya kasance jigo na wani ɓangaren ƙwayar halitta wanda kwakwalwa na ɗauke da kashi 60%.

  Mai karatu na iya duba wannan makala:  Abinci kalar biyar dake kara kaifin kwakwalwa

  Har ila yau, man zaitun na taimakawa wajen kiyaye wasu sassan jijiyoyin jiki. Haka kuma wasu masu bicike a ƙasar Faransa sun gudanar da bincike da suka gano cewa man zaitun na da matuƙar amfani wajen ƙara kaifin basira. Sannan abin da sakamakon binciken ya nuna shi ne, amfani da man zaitun zai taimaka wajen warware harshe da washe maganai (ido) musamman ma ga tsofaffi da suke amfani da man ɗin a kai a kai (lokaci). Sannan man zaitun na taimakawa wajen rage ƙiba musamman ma ga yara 'yan shekaru 13-19 (teenagers.)

  4. Gyaran jiki da gashi

  Matuƙar kana fama da matsalar zubar gashi da lalacewarsa, yawaita amfani da man zaitun, saboda Vitamin da kuma sinadaran antioxidants da ke cikinsa waɗanda suke taimakawa wajen haɓaka sumar kai da ingantashi, sannan ya kare shi daga zubewa nan gaba. Haka kuma man zaitun na samar da sinadarin Vitamin A da Vitamin E waɗanda dukkaninsu ingantattu ne wajen gyara lafiyar fata ta zama sumul ta yi laushi. Sannan sinadarin antioxidants da ke cikin man zaitun ɗin na taimakawa wajen inganta lafiyar tsohon fata ya maida shi tamfar na sabo.

  5. Magance ciwon zuciya

  Bincike da dama da manazarta suka gudanar sun tabbatar da cewa yawaita amfani da man zaitun na rage bugun jini a zuciya, saboda sinadaran da ke cikin man zaitun na tocopherol, polyphenols da kuma wasu sinadaran waɗanda suke taimaka wa zuciya ya numfasa. Kamar yadda bncike da wasu masana kimiyya a Spaniya (Spanish scientists) suka gudanar sun nuna yawanta amfani da manzaituna na taimakawa wajen daidaita numfashi ga tsofaffin mutane. Haka kuma man zaitun a jiki yana rage yawan cholesterol a jikin manyan mutane (tsofaffi) tare da ƙara kare lafiyar jikinsu.

  Waɗannan su ne kaɗan daga cikin amfanin man zaitun ga lafiyar jiki, ko kuma ta ɓangaren abinci ko abin da ya shafi lafiyar jiki. Man zaitun zai taimaka maka wajen inganta rayuwarka.

  Allah Ya bada lafiya. Kuna iya karin bayani ida akwai wani amfani na man zaitun din da kuka sani don sauran masu karatu su amfana da shi.

  Kana kuna iya duba wannan sabuwar makalar kiwon lafiya: Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted Sat at 3:40 PM

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All