Makalu

Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

 • A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani.

  Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ne na kwarai ba, wasu daga cikin matasan namu sun mai da shi tamkar ado. Yayin da za ka ga matashi ko matashiya tana aikatawa tamkar bata san illar da ke cikin abin ba sabo da shaidan ya yi musu hudubar tsiya basa ganin aibun abin.

  Abin tsoron shi ne, ada wannan wata dabi’a ce da muke jinta a nesa ko kuma a tsakanin ‘yan daba, sai ka ji ana labarin abin ana kyamarshi sannan ana mamaki. To yau da kadan-kadan ga shi ya zo ya cimmana har gida. Yaro ko yarinya a gidan iyayensu suna shan wadannan miyagun kwayoyi. Wa iyazu billah!

  Dadin dadawa wannan dabi’a a da dabi’a ce da ake ganin maza ne kawai suke shigarta, abin takaici shi ne yanzu mata da yawa sun shiga kama daga ‘yan mata matasa har izuwa matan aure. Matan har suna neman su kere maza don ana ganin kashi sittin cikin dari na masu shaye-shaye a yanzu mata ne.

  Duba wannan Makala da ya yi nazari akan binciken masana game da shaye-shayen mata a arewacin Najeriya.

  Mata da ake tsammanin za su taimaka wajen gyara dabi’un yara kuma su ma sun bage da shiga wannan hali ai al’amarin ya baci. Duk sanda ake ce mace to ai ana mata kallon uwa ce, kuma ita ce fiye da kowa take da hakkin gyara al’umma. In har mace ta gyaru to ana sa ran al’umma zata gyaru.

  Illolin shaye-shayenan suna da yawa ainun, kama da ga yadda yake jirkita mu su kwakwalwa har zuwa yadda yake bata musu wasu daga cikin vital organs (kamar su huhu da hanta) na su, da kuma maye da ya ke haifar mu su ta inda za su rika aikata wasu abubuwa na ashsha ba’a cikin hayyacinsu ba.

  Kafin na kawo muku bayani game matsalolin da shaye-shaye ke kawo wa, bari na kawo muku sakamakon bincike da muka yi game da dalilan da mutane, musamman matasa mata, ke shiga shan kwayoyi.

  Dalilan dake jawo shaye-shaye

  Mun yi wani bincike da muke so mu gano dalilan dake sanya matan aure ke shiga shaye-shaye, kuma mun samo bayanai kamar haka:

  Rashin kasancewar mazaje kusa ga matansu

  Wata matan aure ta tabbatar mana da cewa ta shiga shaye-shaye ne sakamakon mijinta baya zama a gari. Tun lokacin da ya aureta yakan tafi wata jahar aiki ya barta a gida bawani abokin fira, sakamakon haka ke sata ta sayo maganin mura ta sha domin ta iya bacci, wannan shine sanadiya

  Matsalolin aure

  Wata kuma ta shaida mana cewa bakin ciki ne ya sanya ta shiga shaye-shaye. Mijinta ke muzguna mata, kuma koda ta kai karar sa a gida ba’a ganin laifinsa saboda tun farko an san bata son shi sai ake ganin tamkar sharri take mishi. Sanadiyar haka kawarta ta bata shawarar ta dinga shan kwayoyi in ta tsinci kanta a wannan matsayin.

  Mummunar kawance

  Yawan kawance da miyagun abokai ko kawaye kan kawo shiga shaye-shaye. Idan kai baka sha ko ba ki sha to baki waye ba ko ba lallai bane a yi kawance dake. Har’ila yau, samari na amfani da kwayoyi ga ‘yan mata don cimma wata manufa tasu sakamakon sun san basa samun dammar amfani da matan in bawai sun fita hayyacinsu ba.

  Shiga bangar siyasa

  Akwai matashin da ya shaida mana cewa ya shiga shaye-shaye ne saboda siyasa. Kasancewar s abaya iya daukar wasu hayaniya da matsaloli har sai ya hada da shan kwayoyi, kana ya tabbatar mana cewa wasu a cikin mutanensa duk hakan take faruwa saboda irin gwagwarmayar da suke shiga. Wa su manyan kuma sukan fara ne da shan magungunan kashe gajiya da ciwon jiki, daga nan kuma sai su saba.

  Sanin kowa ne duk wani maganin da za kasha batare da likita ya rubuta maka ba ko kuma baka sha shi a kan ka’idar likita ba to fa ana kiransa da drug abuse, don haka yana dakyau mu kiyaye sosai ko don zaman lafiyarmu, mutuncinmu, da kuma kare addininmu.

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi bayani akan shawarwari 8 don inganta tarbiyan yara.

  Yanzu kuma ga kadan daga cikin manyan matsalolin da shaye-shaye ke jawowa a yau.

  1. Jirkita kwakwalwar mai sha

  A yayin da mutum ya dauki mummunar dabi’a ta shan miyagun kwayoyi, a wannan lokacin tunaninsa zai banbanta da na masu hankali wanda sanadiyyar haka yana haifar da ciwon hauka sannan kuma ya illata wasu sassa na jiki da kwakwalwa. Ya kan koma baya jin kunyar kowa baya kuma jin tsoron kowa.

  2. Matsalolin rashin lafiya

  Mai shaye-shaye kan gamu da cututtuka daban-daban wadanda sun hada da kwakwalwa, ciwon kirji, ciwon koda, ciwon hanta harma ga mata yakan lalata musu mahaifa.

  Kuna iya karanta wannan makala da ta yi karin bayani game da illolin shaye-shaye ga lafiyar jiki, ko kuwa wannan dake bayani akan rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo.

  3. Aikata munanan abubuwa na ashsha

  Tabbas akwai abubuwan da mutum mai hankali ba zai iya aikata su ba sai dole ta hanyar fita hayyacinsa wanda hakan zai sa ya koma amfani da wani tunani na daban kuma ya iya aikata abubuwan ashha ba tare da tausayi ko sanin dai-dai ba. Daga cikin irin abubuwan da mashayi zai aikata sun hada da: aikata kisan kai, fyade, bangar siyasa da sauransu.

  Kuna iya duba wannan makala da ta yi sharhi bisa dalilan dake kawo yawan fyade a yanzu. Shaye-shaye na daga cikin su.

  4. Rasa mutunci da darajar kai

  A yayin da mutum ya dauki shaye-shaye a matsayin abin yi koda yaushe yakan rasa duk wata daraja da kuma mutuncinsa a idon jama’a. Hakan kan jawo ma sa kaskanci da wulakanci a rayuwa.

  5. Shaye-shaye kan nisanta mutum daga ibada

  Sakamakon gushewar tunani da shagalta cikin aikin ashsha sai ka ga lokuta ibada na kubucewa mutum ba tare da mutum ya sani ba. Wannan irin yanayi na kara cusa mutum cikin halin da sai dai a ce Allah Ya gyara.

  Kuma ba zai dace ace mutum ya tsinci kansa a wannan yanayi na shaye-shaye ana kyamatar sa ba ko kuma ana kokarin sa ba wai a nema masa magani ko mafita akan hakan ba. Yana da kyau kuma ya zama dole a gaggauta kai mutum wajen likitoci sannan kuma yakasance an sama abin yi ta yadda ba zai sake fadawa irin wannan hadari ba.

  Muna rokon Allah da ya shiryar mana matasanmu a kan tafarki madaidaiciya. Sannan iyaye da gwammanti ya kamata kowa ya yi iya kokarinsa a matsayinsa wajen rage ko kuma kawar da wannan dabi’a gaba daya a cikin al’umma.

  Wacce ta rubuta: Hadiza Balarabe, daga Kaduna, Nigeria

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

  Posted Oct 19

  Asaalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu duba yadda uwargida za ta hada miyan masa, kuma wannan miyan za ki iya cin abubuwa dayawa ma da ita. Abubuwan hadawa Manja Albasa da lawashi Kayan miya Naman rago Allayaho...

 • Darasi game da electrical method

  Posted Oct 18

  A makala ta da ta gabata mai suna method of mixture na yi bayanin specific heat capacity yanda ya ke dauke da method guda biyu na measuring dinshi wanda na kawo su kamar haka: Method of mixtures Electrical Method Saboda haka method din lissafinsu ma biyu ne, kuma...

 • Yadda ake grilled sandwich

  Posted Oct 18

  Abubuwan hadawa Biredi mai yanka Soyayyen plantain(agada) Kwai Nama (ki dafa, ki daka) Tarugu (ki jajjaga ko ki yanka) Koren wake (ki yanka) Karas (ki yanka) Kabeji (ki yanka) Maggi Gishiri Butter Abun gashi (manual sandwich grill) Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada buttered shape cookies

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum, makalarmu ta yau zamu yi bayani ne akan yadda zaki hada butter shaped cookies Abubuwan hadawa Flour 2 cups Sugar 1 cup Butter 250grm Baking powder 1tspn Kwai 1 Icing sugar Egg white Yadda ake hadawa Farko za ki mixing sugar da butter n...

 • Yadda ake hada red velvet coconut balls

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Zamu yi bayani akan yadda za ki hada red velvet coconut balls a yau. Abubuwan hadawa Kwakwa Condensed milk Madarar gari Corn flour Red colour Yadda ake hadawa Farko za ki zuba corn ...

View All