Makalu

Shin wai menene Bakandamiya?

 • Yan’uwa, barkanmu da warhaka. Mutane da dama sun rubuto suna nuna cewa basu fahimci menene Bakandamiya ba. Mun gode da tambayoyinku.
   
  A takaice, 'Bakandamiya' suna ne da a ka sanya ma wannan dandali wanda da shi za a ke ambatonta da shi.
   
  Tambaya a nan shine wani abu muka zo dashi sabo don Jama’a su karu da shi?
   
  Idan mai karatu ya fahimci menene Facebook ko Twitter, muna ganin ba zai yi wahalar fahimtar Bakandamiya ba. Wadannan kafofi da muka ambata a na amfani da su ne don sadar da zumunci, ilmantarwa da sanin abubuwan dake gudana na yau da kullum a cikin gida da waje. Wasu na amfani dasu don tallata hajarsu, kai harma da siyasa.
    
  Saboda haka abinda ya bambanta Bakandamiya da wadannan kafofi na yanar gizo da muka ambata sune:
   
   
  Na farko: Bakandamiya an kirkiroshi ne dungurungun cikin harshen Hausa ta yadda masu amfani da harshen za su fahimci mu’amala dashi fiye da yadda suke fahimtar sauran.
   
  Na biyu: Kasancewarsa cikin harshen Hausa zai bai wa mutane masu yawa damar bada gudumawarsu a harkokin yau da kullum ta anfani da na’ura mai kwakwalwa.
   
  Daga karshe: Za ku iya amfani da Bakandamiya wajen ‘posting’ hotuna, bidiyoyi, sautuka; za ku iya kirkiro zauruka (wato groups) don musayar basira da wadanda ku ke so. Za ku iya aiko da tambaya a zauren tambayoyi, wadanda masana da dama da kuma sauran mambobi za su amsa muku. Za ku iya sanar da bukukuwa ko tarukanku. A kwai abubuwa da dama da za ku iya yi a Bakandamiya. Idan ku ka yi ragista da sannu za ku fahimci wadannan abubuwa.
   
  Kuma idan kuna da wata tambaya kuna iya aikowa, za mu amsa muku in Allah ya so. Da fatan wannan dan takaitaccen bayani zai fa’idantar.
   
  Mun gode.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All