Makalu

Snell's law: Lissafin refraction

 • Makala ta da ta gabata wadda ke dauke da tarihin snell’s law wadda na yi bayanin cewa Ibn sahl shine mutum na farko da ya kawo wannan Snell's law kamar yadda muka san shi a yau. A bayanin kuma na kawo fomuloli wanda ake amfani da su wajen lissafin refraction. A wannan karon, yanzu zamu dauki misalai daga cikin tambayoyin jarabawar karshen aji a sakandire wato JAMB da WAEC.

  Tambaya ta farko:

  1. A beam of light is incident from air to water "t" an angle of 300. Find the angle of refraction if the refractive index of water is 4/3.  A.50    B.18  C.220      D.240  .      (JAMB 1993)

  Amsar tambaya:

  Zamu fara fitar da abubuwan da aka bamu kamun musan wacce fomula zamu yi amfani da ita

  Data:   

  Angle of incidence,  i = 300

  Refractive index, ∩ = 4/3

  Angle of refraction, r = ?

  Yanzu zamu yi amfani da law na refraction, ga ta kamar haka: ∩ = sin I / sin r

  Data da muka fitar yanzu zamu sa kowannensu cikin fomula kamar haka:  4/3 = sin30 /sin r

  Yanzu zamu yi cross multiply saboda 'r' ta zama subject na fomula

  Sin r × 4 = 3 × sin 300

  Sin r = 3 × 0.5 / 4 = 1.5 / 4 = 0.375

  Yanzu angle of refraction zai zama:  r = sin-1 0.375 = 220

  Saboda haka amsarmu ya zama 'C' ke nan.

  Za a iya karanat: Abubuwan da ya kamata a sani game da mechanical energy da machin

  Tambaya ta biyu:

  1. Light of velocity 3.0 × 108ms-1 is incident on a material of refractive index ∩ . if the velocity of light is reduced to 2.4 × 108ms-1   in the material, what is ∩?    A. 3.33     B.  2.25    C.1.33   D.1.25   (JAMB 1997)   

  Amsar tambaya: 

  Bari mu fara fitarda abinda aka bamu

  Data:

  Velocity of light at incidence Va = 3.0 × 108ms-1

  Velocity of light after refraction Vg  = 2.4 ×  108ms-1  

  Yanzu zamu dauko fomula da zamu yi amfani da ita.

  Refractive index ∩ = Va / Vg = 3.0 × 108 / 2.4 ×  108  = 1.25

  Saboda haka amsarmu shine 'D' ke nan.

  Tambaya ta Uku:

  1. The velocities of light in air and glass are 3.0 × 108ms-1 and 1.8 × 108ms-1. Calculate the sine of the angle of incidence that will produce an angle of refraction of 300 for a ray of light incident on glass.     (WAEC 1988)

  Amsar tambaya:

  Yanzu zamu fara fitar da abubuwanda aka bamu

  Data:

  Velocity of light in Air,  Va = 3.0 × 108ms-1

  Velocity of light in glass, Vg = 1.8 × 108ms-1

  Angle of refraction  r = 300

  Sine of angle incidence, sin I = ?

  Yanzu zamu dauko formula da zamu yi amfani da ita wajan lissafin

  ag  = velocity of light in Air / velocity of light in Glass

  = sin I / sin 300  = 3.0 × 108  / 1.8 × 108

  Zai zama sin i =  sin 300  × 3.0 × 108  /  1.8 × 108  = 0.5 × 3 / 1.8 = 1.5 / 1.8

  = 0.83

  Tambaya ta hudu:

  1. An electromagnetic wave of frequency 5.0 × 1014 HZ is incident on the surface of water of refractive index 4/3. Taking the speed of wave in air as 3.0 × 108 ms-1 , calculate the wavelength of the wave in water. (WAEC 1998)

  Amsar tambaya:

  Data:

  Frequency, f = 5.0 × 1014 HZ

  Refractive index, ∩ = 4/3

  Wave speed, V = 3.0 × 108 ms-1  

  Daga V = λf, wavelength in air,  λ = V / f = 3.0 × 108  /  5.0 × 1014  = 6.0 × 10-7m

  Yanzu zamu dauko formula da zamu yi amfani da ita wajan lissafin kamar haka:

  aw = wavelength of wave in air (λa) / wavelength of wave in water (λw)

  4/3 = 6.0 × 10-7 / λw

  λw =  6.0 × 10-7 / 4 = 3 × 6.0 × 10-7 / 4

  = 4.50 × 10-7 m

  Wadannan tambayoyi misalai kadanne da na kawo muku. Yana da kyau dalibi ya kara karatu  da kuma gwada amsa wasu tambayoyin domin tabbatar da ya fahimci wannan karatun.

  Sannan mai karatu zai iya duba: Linear momentum: Misalin lissafin impulse

  Hakkin mallakar hoto:Byju's

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All