Makalu

Ba mafita ba ce kashe kai a matsayin samun saukin damuwa

 • A yau ina son in yi magana akan wata musiba da ta tunkaro mu wadda idan mu kai wasa tana iya zame mana tamkar annoba a kasar nan. A yayinda wasu ke fafutukar neman abinda za su ci domin ru rayu su da iyalansu, wasu kuma na kwance a asibiti cikin matsananciyar jinya wanda yan’uwansu na tsaye kansu da kuma jajurcewa don ganin sun nemar musu lafiya, haka zalika wasu kuma ke kokarin neman kudin da za su amso yan’uwansu daga hannun masu garkuwa da mutane domin kada a kashe musu su, to amma duk da wannan yanayi na damuwa da mutane daban-daban ke ciki, bai hana wani mummunan musiba ko ince annoba na kisan kai-da-kai kunnowa ba. Allah ka yi mana tsari!

  Duk da wannan wahalhalu da kalubalen da mutane ke fuskanta dangane da neman hanyar da za su bi don ganin sun rayu cikin kwanciyar hankali da lafiya, hakan bai hana wadansu mutanan tunanin neman hanyar da zasu halaka kansu ba, don watakila, a ganinsu wannan hanayar ita ce kawai mafita a gare su. Wa iyazu billah, Allah ka kare mana imaninmu.

  Abinda ke cimin tuwo a kwarya shine yadda wasu matasan ba su dauki rayuwarsu a bakin komi ba. Don rashin imani da juriyar duk wata jarabawa ta rayuwa, har Allah ya yaye musu su sami mafita, sai su dauki cewa hanya mafi sauki itace su kashe kansu da kansu domin su a tunaninsu shine zai sa su sami saukin duk wata damuwa da kuma mafita da duk wani musiba da matsanancin yanayi da suka shiga.

  Tabbas wannan ba karamin kuskure ba ne domin babu addinin da ya halasta cewa mutum ya kashe kansa. Ba addinin da ya ce wadda ya kasha kansa zai mutu dan aljanna kuma zai samu sauki a can fiye da duniya.

  Kafin inci gaba da wannan bayani ina so in baku misalan kisan kai guda uku da aka yi, wanda an yi su kuma kowa ya sani. Waddannan misalai kadanne daga cikin halin Allah wadarai da matasa ke bi don ganin karshen rayuwarsu.

  Misali na daya

  A watarana ne a Zaria wata yarinya ta zo makaranta ta ke gayama kawayenta cewa ta siyo shinkafar bera za ta ci domin ta mutu. Ta ce musu ta gaji da duniyar ne saboda ita ‘yar goyo ce kuma Antin (uwar goyonta) dinta wadda ta takura mata harta kai ga a gida ba dadi a makaranta ma ba dadi.

  Ta ce domin antin na ta tazo ta gaya ma shuwagabannin makaranta cewa ba ta jin magana kuma yawon banza ta ke. Hakan ya sa su kuma a matsayinsu na masu tarbiyya sai suka dauki wata mummunar dabi’a ta siffanta wannan yarinyar da munanan kalamai, hatta in suka ganta da kawaye sai su umurci kawayen da cewa su dena hulda da ita, ai karuwa ce kada ta lalatasu.

  Wannan dalilai suka sa ta ji gara ta bar duniyar kawai domin ba ta da inda za ta ta ji sanyi. A wannan lokacin kawayen suka amshi wannan shinkafar bera suka hana ta. Sai suka yi ragon a zanci ba su sanarwa kowa ba, ashe bayan da ta koma gida ta kara sayan wata. Ai sai gawarta aka gani ta ci ta fadi ta mutu. Allah ya kyauta, aikin gama ya gama!

  Misali na biyu

  A kwai wani lokaci da wata yar bautar kasa cikin garin Kaduna ta zo kasuwa ta sayi maganin kwari na ruwa wanda ba wanda ya yi tunanin sha za ta yi. Bayan ta saya tana kaiwa wani lungu ta sami wuri ta zauna ta bude tasha. Ai ita ma, sai kakarinta aka ji mutane suka zo domin su kawo mata dauki amma ina, kafin kace kwabo, rai ya yi halinsa. Ita wannan ‘yar bautar kasan ba wanda yasan dalilinta na aikata wannan aika-aika wa kanta da ta yi.

  Misali na uku

  A watan December 2018 dinnan da ya wuce ne kuma aka sake samu wani mummunar labarin na wata matashiyar yarinya. Wannanan yarinyar ‘yar makaranta ce, tana karatu ne a jami’ar Ahmadu Bello University da ke garin Zaria. Kuma tana mataki na 300 level ne ma a jami’ar. Wannan yarinyar an same ta ne a mace ta sha maganin kwari ta kashe kanta. Ta bar wasiyya a takadda a yayin da za ta kashe kanna ta. Ta rubuta a wasikar akan cewa mahaifiyar ta ce take kuntata mata harta kai ga tana kiranta da munanan kalamai.

  Za a iya duba: Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Wadannan misalan kadanne daga cikin abubuwan da matasa ke yi yanzu domin subar duniya. Amma tunda ake samun hakan ban ji iyaye sun ta shi tsaye ba wajen ganin an kawo karshen wannan matsalolin da ke faruwa. Ni a gani na wani lokacin irin waddannan abubuwa na faruwa ne sakamokon sa hankalin iyaye da kuma rashin cikakken ilmin addini. Domin kuwa idan har iyaye sun tsaya sun bawa yara ilmi za su san cewa haramun ne ka kasha kanka. Za su san cewa koda ka fi kowa ibada a duniya ne, in har ka kashe kanka, mahaliccinka ba zai amsheka a matsayin mai addini ba sai dai ka tafi a matsayin mara addini wanda wuta ce makomarka. Da wannan na ke ganin ba dalili ba ne da za ka dauki ran kanka saboda wata matsala wadda ba ta kai ta kawo ba.

  Ina son musani cewa duk wata musiba ko matsanancin hali da zamu tsinci kanmu a ciki, jarabawa ce daga mahaliccinmu wanda idan mu kai hakuri zamu ga kamar bai faru ba.

  Abubuwan da ke sa matasa na hallaka kansu

  1. Sakacin iyaye
  2. Hulda da kawaye/abokan banza
  3. Buri da son duniya
  4. Rashin cikakken ilmin addini
  5. Soyayya
  6. Rashin Hankali

  Wadannan kadanne daga cikin abubuwan da ke jawo matasa ko ince ke tunzura su don ganin sun rabu da rayuwar duniya. Zan dauki kadan a ciki na yi bayani akai.

  Sakacin iyaye

  A gaskiya iyayanmu na yanzu musamman na wannan zamanin suna taka muhimmiyar rawa don jefa yaransu cikin wani matsanancin hali wanda haka kankawo barazana ga rayuwarsu ta duniya. Iyaye sukan nuna halin ko inkula akan yaransu tun daga yarantarsu har girmansu. Wasu kuma kan dauki dabi’a ta sangarta yaran har sai yaran suna neman gagaransu, daga baya su ce za su fara kwabansu, to amma sau da dama yaran sun rigaya sun kangare ko bas u sab aba. Garin neman gyara sai yaran su shiga damuwa matsananciya wadda za su fara ganin wadanda ke ba su farincii sun koma makiyansu.

  A duba: Salallan mazan banza don hadaka da matan banza

  Har ila yau iyaye ba su jajircewa don ganin yaransu sun sami ilmin addini sosai kuma susa ido suga yaran suna aiki da wannan ilmin. Da wannan nake jawo hankalin iyaye don ganin sun maida hankali akan amanar da Allah ya ba su akan yaransu. Sannan kuma iyaye maza ina jawo hakulanku akan yawan aure-aure wadda har zai sa su kasa rike yaransu ko kuma su barsu da matansu wanda basu kaunarsu,ya zama suna muzguna musu.

  Hulda da kawaye/abokan banza

  Tabbas wannan kalubale ne babba akan matasanmu domin kuwa koda sun fito gidan tarbiyya in ya zama na abokansu ko kawayansu a makarantu na banza ne hakan na sawa su fada wani mummunan hali, kadan daga cikin wadannan halaye sun hada da:

  1. Shaya-shaye
  2. Satar amsa a jarabawa
  3. Bin matan banza ko samarin banza
  4. Shiga kungiyar asiri
  5. Shiga kungiyar madigo
  6. Shiga kungiyar luwadu

  Wadannan kadanne daga cikin munanan dabi’un da matasa ke dauka atare da abokanan karatunsu ko kawayansu wanda hakan kan jawo su fada matsanancin hali.

  Da wannan na ke jawo hankalin matasa akan su koma ga Allah su sani sune manya gobe. Idan tunda yarantarsu sun shiga irin wadannan munanan dabi’u wanda da yawa a haka suka salwantar da rayuwarsu tabbas ba abu ba ne mai kyau a garesu da al’umma baki daya.

  Buri da son duniya

  A duk lokacin da mutum ya kasance shi me yawan buri ne ta hanyar duk abinda mutuum ya gani sai ya ce shima sai ya mallaka ko kuma mutum ya kasance mai son abun duniya da yawa. Dole ya/ta samu matsaloli domin ko ance, ba ki da gashin wance ai ba ki yi kitson wance ba, haka kuma, ai shi kwadayi mabudin wahala ne. Don haka a wannan hanyar za ku ga ace wai yarinya basu da shi a gidan iyayenta amma ta je tasa kanta ahali wanda tana ganin kota halin kaka sai ta malllaki abu, ko don abokanta suna da mota ko suna kashe ma mata kudi (namiji ke nan) kai ma kace ai ala dole kota yaya sai ka yi hakan kansa ka shiga matsanancin hali wanda sai ya zama mata shi ya shiga halinda yaji gara mutuwa da rayuwa.

  Wadannan suna cikin abubuwan da matasa ke sa kansu a ciki wanda basu rasa ci ba basu rasa sha ba kuma suna da lafiyarsu. Amma saboda sun sa kansu a wani hali sai su ga duniyar tai musu zafi ba sa bukatar rayuwa. A gaskiya yana da kyau mu sani cewa Allah ya halicce mu ne domin mu bauta mi shi. Bai haliccemu domin mu bautama duniya ba, kuma duk wanda ya kashe kansa to fa ya mutu kafiri babu wani rangwame ko gafara wuta za shi.

  Duba: Ba mafita ba ce korar 'ya'ya mata daga gidajen iyayensu

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All