Makalu

Physics: Bayanai game da gas laws

 • A yau zamu yi karatunmu ne na fannin ilmin kimiyyar lissafi akan wani maudu'i mai matukar mahimmanci wato gas law. Shi wannan gas law ana siffanta shine da abubuwa guda uku, gasu kamar haka: volume, da temperature, da kuma pressure.

  Kafin mu fara bayani akan gas law din zamu san abubuwan da suka hadu suka zama gas, pressure din gas shine force wanda gas ke hada gas ya takura shi wuri daya ya zama yana tafiya a perpendicular per unit. Idan muka koma bayani ta fannin lissafi kuma zai zama kamar haka:

  Pressure = Force / Area = mass × acceleration due to gravity / Area

  = density × volume × g / Area

  = density × Area × height × g / Area

  A kula: Yana da kyau mu san wannan: (density = mass / volume) (volume = area × height)

  Pressure = density × height × g

  P = phg (an sanshi da pressure fomula).

  Ana auna pressure da

  N/M2 1.013 × 105N/m2 = 1 atmosphere = 1.013 × 105 Pa = 760mmHg

  A dubaPhysics: Yadda ake lissafin screw

  Gas pressure measurement

  Ana amfani da manometer wanda yana iya zama manometer na ruwa ko na mercury domin auna pressure gas kamar yadda kuka gani a fig 1.0

  Fig 1.0 

  The gas pressure (p) at X = pressure in the liquid at Z

  = Atmospheric pressure + pressure due to water column YZ

  Gas pressure, p = = P + h

  Duba fig 1.1

   

  Fig 1.1

  Atmospheric pressure (P) acting at N = pressure in the liquid at M

  = pressure of gas(p) + pressure due to mercury column LM

  P = p + h

  Yanzu zai zama, pressure of gas, p = P – h

  KarantaSnell's law: Lissafin refraction

  Yanzu zamu dauki misali guda daya wanda ya nuna mana yadda ake lissafin pressure kafin mu fara bayani akan gas laws wanda suma kowannensu zamu kawo shi tare da lissafinsa.

  Misalin lissafin pressure

   

  Fig 1.2

  The water manometer shown above is measuring the pressure of the gas supply. If the specific gravity of mercury is 13.6 and the atmospheric pressure is 70cm of mercury , what is the total pressure of the gas supply in cm of water. (JAMB 1982) A. 67cm B. 73 cm C. 949cm D. 952cm E.955cm

  Amsar bambaya:

  Yana da kyau mu sani cewa specific gravity is the same as relative density.

  Relative density = density of substance (Hg) / density of water.

  Therefore, density of mercury = Relative density of Hg × density water

  = 13.6 × 1000

  = 13600kgm-3

  The equivalent of the atmospheric pressure (70cmHg) in cm of water is calculated by equating pressure formula for water and mercury as follows:

  (phg) water = (phg)mercury

  Yanzu zai zama

  Density of water × height × g = density of Hg × height of Hg × g

  1000 × h × 10 = 13600 × 70 × 10

  h = 13600 × 70 × 10 / 1000 × 10 = 952000 / 1000 = 952cm

  The atmospheric pressure, P = 952cm of water

  Total gas pressure, = Atmospheric pressure (P) + pressure due to 3cm of water

  = 952 + 3

  = 955cm of water

  Wadannan sune kadan daga misalin lissafin pressure, a makalata da zata gabata zankawo muku ire-iren Gas law da lissafinsu

  Sannan a duba wannan a TuranceGas law

  Hakkin mallakar hoto:chem.fsu.edu

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

  Posted Wed at 8:34 PM

  Alfanun tsiro ko ganye a matsayin abinci ko hanya ta samar da waraka (magani) daga wasu nau’o’in cututtuka ga ɗan Adam daɗɗaɗe abu ne a tarihi. Don haka, kusan kowace al’umma ta tanadar da hanyoyin sarrafa nau’ukan abincinta da kuma samar da kari...

 • Bayanai game da Boyle's Law

  Posted Mon at 7:09 PM

  Boyle’s law yana daya daga cikin laws na gas wanda a makala ta da ta gabata na yi bayani akai. Kamar yadda na fada a baya, a yau kuma zamu je kai tsaye ne don duba daya daga cikin gas laws. Wannan law din shine boyle’s law. Wani lokaci akan kira bo...

 • Abubuwan da dalibanmu ya kamata su sani kafin rubuta JAMB, WAEC da NECO

  Posted Apr 12

  A yau za mu ci gaba ne da tattaunawarmu akan jarabawar JAMB da muka faro a baya. Idan mai karatu na bukatar sanin abinda muka yi a baya zai iya duba inda muka tattauna akan Ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta game da jarabawar JAMB. Insha Allah za mu ci gab...

 • Hanyoyi biyar (5) da za a bi don rage damuwa (anxiety)

  Posted Apr 10

  Zamu iya cewa duk wani dan adam da Allah ya hallita a doron kasa yana da wani abinda ya ke tsoro. Wannan tsoro kuwa shine akasarin lokaci ke jawo abinnan da ake kira a Turance da anxiety attack (damuwa mai tsanani) ko kuma panic attack. Anxiety ko damuwa mai tsanani wan...

 • Yadda ake hada apple smoothie

  Posted Apr 8

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada apple smoothie. Abubuwan hadawa Apple (tufa) Sugar ...

View All