Makalu

Bayanai game da Boyle's Law

 • Boyle’s law yana daya daga cikin laws na gas wanda a makala ta da ta gabata na yi bayani akai. Kamar yadda na fada a baya, a yau kuma zamu je kai tsaye ne don duba daya daga cikin gas laws. Wannan law din shine boyle’s law. Wani lokaci akan kira boyle's laws da suna Boyle-Mariotte's law (musamman a kasar France). Wannan law din a karkashin binciken gwaji na gas law tana bayani ne akan yadda pressure na gas ya ke kokarin karewa a yayinda volume na gas din ya ke kokarin raguwa.

  Sunan wannan law din ya samo asali ne daga sunan masanin kimiyya (chemist and physicist), Robert Boyle, wanda shine asalin wanda ya fara amfani da law din a shekarar 1662.

  Ga bayanin boyle's law na wannan zamani a Turance kamar haka:

  the absolute pressure exerted by a given mass of an ideal gas is inversely proportional to the volume it occupies if the temperature and amount of gas remain unchanged within a closed system.

  Sannan kuma idan muka koma ainihin defination na law din a Turance shine kamar haka:

  Boyle’s law states that volume (V) of a fixed mass of gas is inversely proportional to its pressure (P), provided the temperature remains constant.

  Wannan shine law din wanda yanzu zan kawo yadda ya ke a karkashin formula wato yadda za a samu saukin aiki da shi wajen lissafi.

  V α 1/P, yana nufin volume is inversely proportional to the pressure.

  PV = K, wannan yana nufin pressure ayi multiplyin din shi da volume zai zama constant k, wanda P tana matsayin pressure na gas, V tana matsayin volume na gas,sai kuma k yana matsayin constant.

  Wannan equation din yana bayani ne akan product na pressure da volume yana zama constant na mass of confined gas. Yana tsayawa a haka ne idan har temperature din ya zauna a matsayin constant. Idan aka kwatanta substance iri daya a karkashin condition guda biyu law din ana iya expressing dinta a matsayin, P1V1 = P2V2.  Wannan formula tana nuna mana a lokacin da volume ya karu, pressure na gas yana raguwa in proportion. Haka kuma, idan volume na gas ya ragu, presssure na gas din yana karuwa.

  Yanzu zamu dauki misalai mu ga yadda ake lissafi tare da wannan formula.

  Misali na farko:

  • A fixed mass of gas at a pressure of 650mmHg occupies a volume of 30cm3.what will be the volume of the gas at 760mmHg if the temperature remains constant?

  Amsar tambaya:

  Wannan tambaya tana nuna mana gas wanda ya ke dauke da mass yana da pressure 650mmHg wanda ya mamaye volume 30cm3 . Tambayar da ake mana anan ita ce meye zai zama volume din gas din a 760 mmHg idan ya zama temperature din ya tsaya a constant,

  Yanzu zamu fara fitar da data,

  Data:

  Initial gas pressure, P1 = 650mmHg

  Final gas pressure, P2 = 760mmHg

  Initial gas volume V1 = 30cm3

  Daga P1V1 = P2V2, final gas volume, V2 = P1V2 / P2

  V2 = 650mmHg × 30cm/ 760mmHg  = 25.66cm

  Misali na biyu:

  • A gas at a volume Vin a container at pressure Pis compressed to one fift of its volume. What will be its pressure if it maintains its original temperature T?
  1. P/ 5  B. 4 / 5 PC. P0  D.  5 P0 (JAMB 1999)

  Amsar tambaya:

  Data:

  Initial gas pressure, P= P0

  Initial gas volume, V1 = V0

  Final gas volume, V2 = 1 / 5V0

  Yanzu zamu dauka daga PV= PV2, final gas pressure, P= PV1 /V2  

  P2 = P0V0 / 1/5V0 =P0V0 /1/5V0 = P0V0 ×  5V0   5 P0                        

  Application of Boyle’s Law to Gas Trapped in a Cylindrical Tube by a Column of Mercury

  Zamu yi bayani ne akan application na boyle’s law akan gas wanda ya ke a cikin cylindrical tube daga column of mercury. Idan tube na uniform cross-section ya kulle a wani lungu yana dauke da fixed mass na gas ko na iska wanda an datse shi da column na mercury mai dauke da length X cm, pressure da ke jikin gas din ya danganta ne da plane of inclination na tube din  kamar yadda yake a zanen fig 1.0

  1. Vertically, with closed end at the bottom

   

  Fig 1.0

  Pressure, p , na gas ya samu ne sakamakon sum na pressure exerted by X cm column of mercury  da kuma atmospheric pressure,P .

  Sakamakon haka za su zama, p = P + X (cm Hg). 

  2. Inverter with open end underneath

   

  Fig 1.1

  Gas pressure p ya samu ne sakamakon banbancin atmospheric pressure (P) da kuma pressure exerted by X cm column of mercury.

  Sakamakon haka za su zama , p = P – X (cm Hg) 

  3. Horizontally

  Fig 1.2

  The gas pressure, p is due ONLY to the atmospheric pressure P, saboda  idan tube din yana horizontal position, the column of  mercury exert very negligible pressure akan gas. Saboda haka zai zama,  p = P (cm Hg)

  Generally, gas volume = length of column of gas (y) × cross-sectional area (A) of the tube.

  Don haka gas volumes na fig a, b, c za su zama y1A, y2A, y3A cm3  .

  Sun zama haka ne sakamakon cross sectional area na tube is uniform kuma duk daya ne a kowanne case, volume na gas ana daukar sa a matsayin length na column din gas. Shine ake nufi da volume V is proportional to length y.

  saboda haka volume din gas na fig 1.0 shine y1 cm

  volume din gas na fig 1.1 shine y2cm3

  volume din gas na fig 1.2 shine y3 cm.

  Za a iya dubaPhysics yadda ake lissafin screw

  Boyle’s law  (P1V1 = P2V2   ) can be applied in deriving a relationship between fig 1.0 and 1.1 yanzu zaku ga ta yadda ake fitar da formula wadda ke dauke da dangan takar dake tsakanin fig 1.0 da 1.1 a zanen da zai gabata da kuma ta hanyar nuna su a lissafi.

  4. Fig 1.3

  1. Vertical
  2. Inverter

   

  Daga zanen fig 1.3a

  1. Initial or vertical pressure, P= P + X

  Initial or vertical volume, V1 = y1A

        Daga fig 1.3 b

  1. Final inverted pressure, P= P – X

  Final or inverted volume, V= y2A

  Yanzu zamu yi substituting dinsu a cikin Boyle’s law P1V1 = P2V2    shine zai bamu

         (P+X )y1A = ( P-X )y2A

  Yanzu zamu yi dividing both side by A, shine zai bamu

  (P+X)y1   = (P-X )y2

  Tunda mun yi deriving wasu formula da ake amfani dasu wajan lissafin boyle’s law yanzu zamu dauko wata tambaya cikin tambayoyin da ake ma daliban sakandire ta karshen karatunsu wato a jarabawa, kamarsu WAEC mu amsa ta tare da amfani da wadannan fomulolin da muka koya a baya.

  Misali na uku:

  A uniform capillary tube closed at one end contained dry air trapped by a thread of mercury 8.5 × 10-2m long. When the tube was held horizontally, the length of the air column was 5.0 × 10-2m, when it was held vertically with the closed end downwards, the length was 4.5 × 10-2m . Determine the value of the atmospheric pressure. [ g = 10m/s-2, density of mercury = 1.36 × 104kgm-3].    WEAC 2004

  Amsar tambaya:

  Abinda ya kamata mu fara yi shine mu fitar da zane wanda a kai mana bayaninsa a wannan tambayar hakan zai sa musamu saukin lissafi mu kuma gane mai muke so mu nemo.

   

  Fig 1.4

  Yanzu tunda mun ga yadda suke a zanan, zamu wuce kai tsaye mu fitar da data.

  At horizontal position, gas pressure is due only to atmospheric pressure, P.

  Daga fig 1.4a, above, Horizontal gas pressure, P 1 = P

  Horizontal gas volume, V1 = 0.05A

  Where A is cross sectional area.

  At vertical position, gas pressure is due to atmospheric pressure + pressure due to mercury column.

  From fig 1.4b above, vertical gas pressure, P2 = P + 0.085

  Vertical gas volume, V2 = 0.045A

  Yanzu zamu sasu cikin boyle’s law

  Substituting into boyle’s law, P1V1 = P2V2  , we obtain

  P × 0.05A = (P + 0.085) × 0.045A

  Divide both sides by A

  P × 0.05 = (P + 0.085) × 0.045

  0.05P = 0.045P + 0.003825

  0.05P – 0.045P = 0.003825

  0.005P = 0.003825

  P = 0.003825/0.005 = 0.765mHg

  The atmospheric pressure (0.765mHg) so obtained is in length of mercury and has to be converted to N/mor Pa using the pressure formula, P = ρgh.

  Given values: density of mercury, ρ = 1.36 × 104kgm-3; g = 10m/s2

  Calculated value: height of mercury, h = 0.765mHg

  Therefore, atmospheric pressure, P = ρgh

  = 1.36 × 104kgm-3 × 10 × 0.765

  104040Nm-2 or 1.04 × 105Pa

  Wadannan sune kadan daga cikin misalan lissafin boyle’s law,yana da kyau dalibi ya kara bincike sosai da kuma amsa wasu tambayoyin domin kwarewa a wannan topic. Allah Ya sa mu dace, amin.

  Mai karatu na iya duba: lissafin weight of a body akan lift da sauransu. 

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): googlegalaxysecience

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All