Makalu

Bayanai game da Charle's Law

 • Charle’s law na daya daga cikin laws na gas wanda a makala ta da ta gabata na yi bayani akai. Yau kuma zan yi bayani ne, kamar yadda na ambata a baya, akan daya daga cikin gas law din wato charle’s law. Wannan law din ya samo sunansa ne daga wani masanin kimiyya mai suna, Jacques Charles.

  Ga bayanin Charle’s law a Turance kamar haka:

  The volume of a given mass of an ideal gas is directly proportional to its temperature on the absolute temperature scale (in Kelvin) if pressure and the amount of gas remain constant; that is, the volume of the gas increases or decreases by the same factor as its temperature.

  Sannan kuma daliban sakandire akan yi musu stating dinshi a Turance cikin sauki da fahimtarsu kamar haka:

  Charle’s law states that volume of a given mass of gas at a constant pressure is directly proportional to its absolute temperature. Wannan law din ana amfani da ita ne akan ideal gas held at a constant pressure ta inda volume da temperature ne kawai suke iya canzawa. Gashi kuma a fomula kamar haka:

  V α T or V / T = constant

  Don haka zai zama V1 / T1 = V2 / T

  V1 = initial volume

  T1 = initial absolute temperature

  V2 = final volume

  T2 = final absolute temperature

  Wanda V1 da T1 initial volume ne da initial temperature wato volume da temperature na farko ko muce na ainihi, wanda kuma V2 da Tsune final volume da final temperature na gas gaba daya.

  Akwai abinda ya kamata mu sani wajan lissafin charles law shine temperatures are absolute temperatures, ana measuring dinsu da Kelvin ne ba da  0C ko 0F kuma yana da kyau koda yaushe a rika converting 0C zuwa K ta hanyar adding 273

  Yanzu zamu dauki misalai da zamu amsa su tare da amfani da Charle’s law wanda zamu dauko sune daga jarabawar karshen gama sakandire wato (WAEC,NECO JAMB).

  Za a iya dubaBayanai game da boyle's law

  Misali na daya:

  • The volume of a given mass of gas is 40cm3 at 27 0 what is its volume at 90 0C if its pressure remains constant?      NECO 2003

  Amsar tambaya:

  Zamu fara fitar da data tukunnna

  Data:

  Initial gas volume, V1 = 40cm3

  Initial gas temperature, T1 = 27 0C = (27 + 273) = 300

  Final gas temperature, T= 90 0C = (90 + 273) = 363K

  From V1 / T1 = V2 / T2, Final Volume, V2 = V1T2 / T1 = 40 × 363 / 300 = 48.40cm3

  Ina kara tunasar da ku akan canza 0C zuwa K tare da kara 273 kamar yadda kuka ga na yi wajan amsa wannan tambayar.

  Misali na biyu:

  • Dry oxygen is trapped by a pellet of mercury in a uniform capillary tube which is sealed at one end. The length of the column of oxygen at 27 0C is 50cm. If the pressure of the oxygen is constant, at what temperature will the length be 60cm.        WAEC 1998

  Amsar tambaya: 

  The volume of the gas is assumed to be proportional to the length of the column of gas, i.e V α l

  Initial gas volume, V1 = 50cm

  Initial temperature, T1 = 27 0C = (27 + 273) = 300K

  Final gas volume, V2 = 60cm

  Tunda munfitar da data bari mudauko fomula musa muyi lissafin.

  Daga wannan fomula V1 / T1 = V2 / T2,

                 Final gas volume, T2   = T1V2 /V2 = 300 × 60 / 50 = 360K or 87 0C

  Misali na uku:

  • A fixed mass of gas of volume 600cmat a temperature of 27 0C is cooled at constant pressure to a temperature of 00C. What is the change in volume?              WAEC 1991

  Amsar tambaya:

   Data:

  Initial gas volume, V1 = 600cm3

  Initial gas temperature, T1 = 27 0C = (27 + 273) = 300K

  Final temperature, T2 = 0 0C = (0 + 273) = 273K

  Daga V1 / T1 = V2 / T2  ,

  Final Gas volume, V2 = V1T2 / T1 = 600 × 273 / 300

  = 546cm

  Change in volume = volume at 27 0C  - volume at 0 0

  i.e = V1 – V2 = 600 – 546 = 54cm3

  Duba: Lissafin inclined plane

  Misali na hudu:

  • A gas occupies a certain volume at 27 0C. At what temperature will its volume be doubled assuming that its pressure remains constant? NECO 2000

  Amsar tambaya:

  Data:

  Initial gas temperature, T1 = 27 0C = (27 + 273) = 300K

  Initial gas volume, V1 = V

  Final gas volume, V2 = 2V (Its volume be doubled)

  Zamu sa values din da aka bamu a cikin wannan fomula V1 / T1 = V2 / T2   shine zamu samu

   V / 300 = 2V / T2 therefore, T2 = 300 × 2V / V = 300 × 2 = 600K or 3270C

  Misali na biyar:

  • A gas occupies 221cm3 at a temperature of 0 0C and pressure of 760mm Hg. What will its volume be at 1000C?.

  Amsar tambaya:

  Tunda pressure is constant kuma mass din baya canzawa,don haka munsan zamu iya applying Charle’s law. Idan muka duba tambayar temperature anbamu ne a celcius, don haka yanzu sai mun fara canza su zuwa absolute temperature (Kelvin)

  V1 = 221cm3; T= 273K (0 + 273); T2 = 373K (100 + 273)

  Yanzu zamu iya sa values din a cikin fomula domin samun amsa

  V1 / T1 = V2 / T2

  221cm/ 273K = V2 /373K

  Rearranging the equation to solve for final volume

  V2 = (221cm3) (373K) / 273K

  V2 = 302 cm3

  Wadanan sune kadan daga cikin misalai na lissafin charle’s law wanda yana da kyau mutum ya kara bincike ta hanyar karanta wasu text book na physics sannan kuma tare da amsa wasu tambayoyin domin fahimta da kwarewa akan lissafi.

  Za a iya dubaYadda ake lissafin screw 

  Hakkin mallakar hoto (photo credit): Socratic.org

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • GARIN NEMAN GIRA

  Posted Nov 1

  GARIN NEMAN GIRA...!* *ZULAIHAT HARUNA RANO* Ya faru a gaske. Cikin nutsuwa ta miƙe tana naɗe sallayar da ta yi sallah a kai, bakinta yana motsin da ke nuni da addu'a take yi. A hankali ta kai dubanta kan ƙaton agogon bangon falon, wanda ya nuna mata karfe goma...

 • Ra'ayoyin mazan Arewa game da kayan ni’ima na mata

  Posted Oct 31

  Bayan ra'ayoyin mata da mu ka ji da irin alfanu da kuma rashin alfanu da kayan mata ke da shi wanda mu ka tattauna a makalar da ta gabata, to yau kuma za mu kawo muku bayanin bincike da na yi dangane da ra’ayoyin maza akan lamarin. Mun ji ra'ayoyi ma bambanta kwar...

 • Yadda ake hada ring chocolate cookies

  Posted Oct 31

  Barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau zamu gabatar da yadda za ki hada ring chocolate cookies(doughnut cookies). Abubuwan hadawa Flour Sugar Butter Kwai Cocoa powder Chocolate chips Baking powder Yadda ake hadawa Farko za k...

 • Yadda ake hada coconut pound cake

  Posted Oct 31

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin girke-girke na Bakandamiya. A yau zamu yi bayani ne akan yadda ake hada coconut pound cake. Sai a biyo mu dan jin yadda ake hadawa. Abubuwan hadawa Kwakwa (desiccated) Kwai 8 Butter 1 (250g) Sugar kofi 1...

 • MA'AURATA

  Posted Oct 29

  ????????????????????  *MA AURATA*????????????????????????????   *By Aisha Abdullahi*Tsaye take abakin ƙofa sai cika take tana batsewa tana jijjiga ƙafa wani matashi ne wanda bazai haura shekara 30 zuwa da 34 ba naga ya buɗe ƙofar da take tsayeDa sauri ta ...

View All