Makalu

Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

 • A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza harda mata a wannan zamani.

  Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ne na kwarai ba, wasu daga cikin matasanmu sun mai da shi tamkar ado. Ya yin da za ka ga matashi ko matashiya yana yinta tamkar bai san illar da ke cikin abin ba, sabo da shaidan ya yi musu hudubar tsiya basa ganin aibun abin.

  Abin tsoron shi ne ada, wannan wata dabi’a ce da muke jinta a nesa muna ko kuma a tsakanin ‘yan daba, sai ka ji ana labarin abin ana kyamarshi sannan ana mamaki. To yau da kadan kadan ga shi ya zo ya cimmana har gida, yaro ko yarinya a gidan iyayenta ya na ko tana shan wa’yannan muyagun abin, wa iyazu billah!

  Dadin dadawa wannan dabi’a a da dabi’a ce da ake ganin maza ne kawai suke shigarta, abin takaici shi ne yanzu mata da yawa sun shiga kama daga ‘yan mata matasa har izuwa matan aure. Matan har suna neman su kere maza don ana ganin kashi sittin cikin dari na masu shaye shaye a yanzu mata ne.

  Mata da ake tsammanin za su taimaka wajen gyara dabi’un yara kuma su ma sun bage da shiga wannan hali ai al’amarin ya baci. Duk sanda ake ce mace to ai ana mata kallon uwa ce, kuma ita ce fiye da kowa take da hakkin gyara al’umma. In har mace ta gyaru to ana sa ran al’umma zai gyaru.

  Illolin shaye shayenan suna da yawa ainu, kama da ga yadda yake jirkita mu su kwakwalwa har zuwa yadda yake bata musu wasu daga cikin vital organs (kamar su huhu da hanta) na su, da kuma maye da ya ke haifar mu su ta inda za su rika aikata wasu abubuwa na aca ba’a cikin hayyacin su ba. Matsalolin  ba su kirguwa.

  Muna rokon Allah da ya shiryar mana da matasanmu a kan tafarki madaidaiciya, sannan iyaye da gwammanti ya kamata kowa ya yi iya kokarinsa a matsayinsa wajen rage ko kuma kawar da wannan dabi’a gaba daya a cikinmu al’umma.

  Za ku iya duba makalunmu da suka shafi rayuwa, tarbiya da zamantakewa, kamar shawarwari 8 don inganta tarbiyan yara da  abubuwan dake ruruta wutar fyade cikin al'umma ko dai rushe tarbiya ta duniyar yanar gizo da ma makamantansu duk a cikin Bakandamiya.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All