Makalu

Bin na gaba bin Allah, in ji masu iya magana

 • Girmama na gaba ɗabi’a ce da ake bukatar ta ga duk wani ɗan adam dake cikin al'umman dake cikin ta, ma'ana 'ya'ya su girmama iyayen su, hakanan mabiya su girmama shuwagabanninsu ko jagororinsu. ‘Bin na gaba bin Allah,’ in ji masu iya magana.

  Ya tabbata cewa biyayya na yiyuwa ne idan su na saman najin tausayin na ƙasa. Abin nufi anan shine, in da ace dukkanmu muna girmama juna kuma muna girmama tunanin junanmu to baza mu ke ganin munin ɗabi'ar junan mu ba.

  Alal misali, kaman gairmamawan da ake bukata daga 'ya'ya zuwa iyayen su, shine su dinga jin maganganunsu kyawawa suna aiki dasu. Dukkan abinda uba ko uwa suka umurci 'ya'ya matukar wannan al'amari ba zai saɓawa addini ba ko da zai cutar da rayuwarsu, wannan umarni ya zama wajibi ne ya bishi domin idan ka zama mai girmama umarnin iyayenka ko yayyinka, to kaima wadanda za su zo a bayanka za su zama suna girmamaka.

  Ba zaka taɓa ganin al'umma ta ruɗe ta shiga wata hanya da babu mai gayamata ta jiba kaman yanda muke ciki a yau. Al'umman da muke raye yanzu kowa gaba gadi yake tafiya babu ruwansa da jagora mai yace domin shi baya girmama shi kuma shima jagoran baya girmama mutuncinsa.

  Mai karatu na iya duba: Ba abinda gaggawa ke haifarwa a rayuwa sai dan da na sani

  Da zamu kawar da kanmu daga wannan kyakkyawar ɗabi'a ta girmama magabata to muma lokacin da girma ya riskemu, anan zamu yi nadamar abinda muka aikata a baya na rashin girmama magabatanmu.

  Hakazalika al'umma su girmama shuwagabanni matukar shuwagabannin nan basu cutar da su ba wajibi ne. Shuwagabannin nan sarakuna ne ko malamai ko kuwa masu rikon mukamai na siyasa. Idan ɗan adam ya san ana girmama shi a cikin al'amuran sa zuciyarsa zata fara tausaya wa al'umman da yake mulka. Amma idan muka kasance bamu ganin girman na sama da mu shima na sama da mu baya ganin girman na sama da shi to abin zai zama tamkar matattakala na rashin imani da tausayawa juna. Idan girmamawa ta ratsa sai ya zama ina ganin girmanka kaima kana ganin girmana, sai tausayin juna ya shiga tsakani.

  Wannan ba mafita bace a rayuwarnan da muke ciki, muyi ƙokari da girmama na sama da mu sai na ƙasa damu su girmama mu, sai kuma a samu tausayin juna da adalci a tsakani. Sannan za a iya karanta: Ni'imomin dake cikin wadatar zuci da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All