Makalu

Dabarun hana haihuwa da illolinsu

 • Akwai hanyoyi ko dabaru da dama da ake bi wajen hana haihuwa, daga ciki akwai:

  1. Kwayoyin magani na hana haihuwa
  2. Allurar hana haihuwa
  3. Zaren mahaifa
  4. Robar mata

  Kwayoyin magani na hana haihuwa (oral contraceptives pills)

  Wadannan kwayoyi ne wadanda ake amfani da su don hana haihuwa. Asalin irin wadannan kwayoyi suna yin tasiri ne ga maniyyin mace su hana su aiki. Daga cikin wadannan kwayoyi akwai wanda ake kira "ancullor," akwai "lyndiol," akwai kuma "liynovlor" da sauransu.

  Wannan dabara na hana haihuwa, likitoci sun bayyana yana yiwa mata illoli ta hanyar farar da al'ada ba a kan ka'ida ba. Watau ba sai lokacinta ya yi ba, ko ma haila ta ɗauke gabaɗaya. A wani lokaci ma amfani da su yakan hana haihuwa dungurungum.

  Allaurar hana haihuwa (projestine injection)

  Ita kuma wannan allura ce da akan yi don hana haihuwa. Daga cikin alluran da aka fi amfani da su don wannan aiki akwai kamar su "Depo-provera medroxy progestere Actate (DPMPA) da "Nokethindrone Enonthate (NET) da sauransu. Ita wannan allurar tana hana ciki ne ta wajen danne karfin kwayoyin maniyyi na mace. Tana kuma kade jikin mahaifa ta yadda ko da ba ta yi tasiri ba kwan maniyyin ba zai sami inda zai makale ba a mahaifa. Tana kuma tara majina mai kauri a hanyar da maniyyi kan wuce zuwa mahaifa, don kada ya samu wucewa.

  Ita ma wannan hanyar na da illoli kwarai. Bincike ya nuna cewa irin wadannan allurai da ake yi kan cutar da jariri idan aka yi su ga mace mai ciki. Za kuma su iya zama sanadin cutar 'cancer', wadda aka fi sani da ciwon sankara ta mahaifa ko ta nono. Akwai kuma cutukan da suka shafi zuciya da hanyoyin jini, irin su: toshewar hanyar jini wadda ka iya jawo ciwon zuciya (heart attack) da hauhawar jini (hypertension) da sauransu.

  Zaren mahaifa (Intra Uterine Devices (IUD)

  Ita ma wata hanyar ce ta hana haihuwa wadda Richter da Graefenberg suka kago a shekarar 1909. Wani zare ne na roba wanda akan sanya a mahaifa a bar shi sai zuwa wani dogon lokaci. Ba za a cire ba sai sanda matar ke son ta sake haihuwa. Wannan zare yana hana maniyyi kuzari ya kuma kashe kwayoyin maniyyi na mace da kwaroron da sukan bi zuwa mahaifa.

  Akwai tabbacin cewa zaren mahaifa na haifar da babbar matsala ga mace, domin yakan farar da yawan zubar da jini, wanda ka iya farar da rashin jini a jiki. Yana farar da bari 'miscarriage' da cutukan da suka shafi mara.

  Robar mata (diaphragms and cervical caps) 

  Ita kuma wata roba ce mai tattausan baki. Wani likita ne a kasar Jamus mai suna Ferick wilde ya kago shi a shekarar 1838. Ana sa wannan roba ne a cikin farji kafin saduwa. Ta yadda zai je ya toshe kofar mahaifa. Ana kuma shafa wani mai wa roban kafin a sa.

  Masana harkar dakatar da haihuwa sun nuna cewa amfani da robar mata kan haifar da wasu munanan cutuka. Misali; yana haifar da saukowar mahaifa, yana farar da cutuka da suka shafi mafitsara (cystitics), kamar yadda yakan farar da zafi a hanyar da fitsari kan bi (urethritis).

  Wadannan kadan kenan daga cikin dabarun da akan yi amfani da su don hana haihuwa. Ba a ma yi maganan riga ba, wato kororo roba (condoms), wanda maza kan sa a azzakarinsu da kumfa (foams) wanda mata kan sa. Akwai kuma hanyoyi da ake bi a dakatar da haihuwar gabadaya, wanda ake kira "STERILIZATION."

  Duk wadannan dabaru da muka ambata dabaru ne wadanda ilimin likitanci ya kago, wadanda imma dai su zama na sha, ko kuma na sanyawa da wani abu, ko ta hanyar allura. Wadannan dabarun Kenan.  

  A biyo mu a makala ta gaba za mu kawo wasu dabarun da kuma yadda suke yi wa mata har ma da maza illa. Mai karatu na iya karanta: Tsarin zaman iyali gandu na al'ummar Hausawa da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted Sat at 3:40 PM

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All