Makalu

Tsarin zaman iyali (gandu) na al'ummar Hausawa

 • Zaman iyali ya kumshi zama ne na mutum da matarsa ko matansa da 'ya'yansa. A tsarin zaman Hausawa na gargajiya, magidanta suna bin tsarin zaman gandu ne wanda yakan kasance zaman babban gida da ya kunshi sashin maigida, da sashin kannensa da 'ya'yansa, su ma wasu daga cikinsu magidanta ne, watau suna da nasu iyalin. Saboda haka shi kansa gandun zama ne na iyalin babban maigida, amma a cikin gandun akwai kananan masu gida da iyalansu.

  Wato kenan bisa ga al'ada, iyalin Bahaushe ba kurum sun kunshi matansa da 'ya'yansa ba ne, a'a, har ma da duk wani wanda yake karkashin ikonsa, ko sun hada dangantaka ta jini, misali kamar 'yanuwansa, da sauran danginsa da 'ya'yansu, ko kuma ba su hada dangantaka ta jini ba, misali matan 'ya'yansa, da barori ko yaran gida, da 'yan aikin gida. A tsarin zaman gandu duk iyalansa ne. Shi babban maigida, wanda akan kira da Babangida, ya zama uba ga wasu mutanen gida kuma kaka ga wadansu.

  Tsarin zaman iyalin Hausawa ya yi daidai da na Larabawa, wanda hakan ba abin mamaki ba ne sanin cewa da dama daga cikin al’adun na Hausawa ya surke da na Larabawa din. Haka kuma wannan al’ada ya sha bamban da na Turawa.

  A takaice za mu iya cewa, kalmar nan iyali, suna ne da ya kunshi dukkan mutanen da ke zaune a 'gida' ko 'gandu' guda a karkashin shugabancin maigida. Sannan mai karatu na iya duba: Dabarun hana haihuwa da illolinsu da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All