Makalu

Hadin fanke na musamman

 • Abubuwan hadawa 

  1. Flour
  2. Yeast/Baking powder
  3. Suga
  4. Kwai
  5. Madarar gari

  Yadda ake hadawa

  1. Ki tankade  flour ki zuba a kwano.
  2. Ki sa yeast da baking powder da madarar gari.
  3. Ki sa suga da kuma kwai,  sai ki dama da ruwan dimi.
  4. Kada ki cika ruwa kuma kada ki yi kwauron ruwa.
  5. Ki buga sosai ki saka a rana ko guri mai dimi ki barshi kamar minti 30
  6. Sai ki soya a ruwan mai. In ya yi za ki ga ya yi brown, shi ke nan sai a kwashe. Haka za ki ta maimaitawa har ki gama.

  Akasari ana amfani da fanke ne wajen karyawa, sannan ana iya cin sa da kunu ko da shayi, ko dai da duk abinda mutun ke so.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

 • Kin yi ta saurare ki ji ya turo manyansa zuwa gidanku amma har yanzu shiru: Ga dalilai

  Posted Jun 29

  Mata mu kan fada cikin yanayi na yaudara cikin sauri ba tare da mun farga ba. Musamman idan namiji ya zo da batun auren ki zan yi, mu kan mika duk wata ragamar rayuwar mu a gare shi, muna masu amanna da mika wuya dari bisa dari.  Sam bama hangen da mi yazo a lokac...

View All