Makalu

Yadda ake dambun Shinkafa

 • Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Zogale
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Maggi/Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida zata wanke shinkafarta ta shanya ta.
  2. Bayan ta bushe sai ta bayar akai Inji a barzo mata.
  3. Idan an kawo sai ta samu rariya ta tankade barjajjjiyar shinkafar.
  4. Ta fitar da dusar, ita kuma shinkafar sai ta yayyafa mata ruwa.
  5. Ta zuba a madambaci ta dora a wuta, a barta tayi ta turaruwa sai an tabbatar tayi laushi.
  6. Sai uwargida ta sauke dama ta yanka albasa da attarugu,sai a zuba akan shinkafar.
  7. Ta kawo zogalenta da aka riga aka gyara shima ta zuba akai .
  8. Anan sai uwargida ta saka magi da gishiri da mai, ta cakuda yadda zai hade jikinsa
  9. Sai ta sake mayarwa kan wuta ya kuma turara, in ya yi za a ji yana ta kamshi.
  10. Idan uwargida tana so zata iya saka gyada a ciki

   Na gode, sai mun hadu a girki na gaba. Sannan za a iya duba yadda ake: Danbun nama da Dambun masara da ma makamantansu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): Naija Food Dot Com

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All