Makalu

Alamomin shugaba na gari

 • Babu al'ummar da za ta ci gaba sai da shugaba ko shugabanci na gari. Shin ta yaya za mu gane alamomin shugaba na gari ko kuwa wanda za mu yi zaton shugabanci na gari daga gareshi. Wannan yana da muhimmanci kwarai musamman a halin yanzu da yan siyasa ke anfani da hanyoyi daban-daban don cinma burinsu, amma kwalliya bata biyar kudin sabulu ga yan kasa.

  Ga kadan daga cikin siffofin shugaba na gari:

  Kamala da kyau manufa

  Duk shugaba in dai nagari ne yana da kamun kai, wato yakan kasance mai nisantar da kai daga wasu dabi’u dake durkushe kima cikin al’umma, misali, yawan shaye-shaye, da neme-nemen mata, da fadace-fadace ko zage-zage. Haka kuma shi shugaba na gari yana da manufa mai kyau akan al’uma. Za a fahinci hakan ne ta hanyar dubi ga yanayin rayuwarsa a cikin mutane da karfin tausayi da yake da shi.

  Hukunci da hukuntarwa

  Shugaba na gari zai gina tsarin mulkinsa akan dokokin kasa da tabbatar da hukunta duk wanda ya take doka. Da farko dai, shi zai zamo mai bin dokan. Yin haka shi zai ci da kasa gaba maimakon kowa ya zama mai daukan doka a hannunsa.

  Za a iya karanta: Sirrantattun matsaloli dake kawo cikas a shimfidar aure

  Natsuwa da Hangen nesa

  Duk lokacin da aka wayi gari shugaba bai da natsuwa, babu ko shakka mulkinsa zai kare abirkice. Komi na bukatar tunani don dora komi akan muhalli da ya dace. Hakan na nuni da cewa shugaba na da baiwa na hangen nesa yanda zai ci da al’ummarsa gaba.

  Rashin tsatsauran ra’ayi

  Tsasauran ra’ayi a nan na nufin yanke hukunci dake da alaka da tunaninsa shi kadai. Irin wannan ra’ayi shike haifar da mulkin kama karya, mulki da talaka bai da ‘yancin baiyana kukansa.

  Girmama karfin mulki

  Mu sani cewa duk shugaban da yake girmama matsayin sauran ma’aikata dake aiki a karkashinsa, shugaba ne nagari. Hakan na nufin zai iya baiwa kowa hakkin aikinsa da daraja daidai da yanda karfin doka ta ba shi.

  Halaye da za mu gane shugaban kwarai suna da yawa. Wannan dan kadan na kawo daidai gwargwadon fahimtata. Allah ya albarkacemu da shugabanni na gari. Amin. Sannan za a iya duba: Abubuwan dake durkushe baiwa da basirar yara da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All