Makalu

Ko ka/kin san hangen nesa tamkar linzami ya ke ga rayuwa?

 • Sakon mu na yau shine hangen nesa. Ko kasan me ake kira hangen nesa? Ko kasan hangen nesa tamkar linzami ne mai iya seseta rayuwa? Ko ka kuma san da cewa hangen nesa shi ke taimakawa wajen daidata rayuwa?

  To, idan baka sani ba, hangen nesa na nufin ka yi kyakkyawan nazari da tunani mai zurfi don baiwa kwakwalwarka damar shari’antar da abinda ake tunani gobe zai haifar; wanda yin haka daidai yake da tubalin inganta rayuwarka ta nan gaba. Ayayin da ka sami dama wajen inganta rayuwarkan, matakai da kabi wajen cimma wanna shi ake nufi da ‘kundin rayuwa.

  To ko meke kunshe cikin kundin rayuwarka? Kuma ta yaya zaka tsara kundin rayuwar taka?

  Amsa a nan itace, komi na kunshe cikin kundi rayuwa. Abin nufi anan shine, zaka sami farin ciki zaka sami bakin ciki, za ka sami dacewa zaka sami rashin dacewa, za ka sami kalubale zaka sami nasara, za ka sami karbuwa zaka sami rashin karbuwa, za ka sami daukaka ko sabanin hakan. Haka za ka sami kudi ko kishiyar hakan. Babban abin da ake bukata anan shine ka kasance mai manufa da tsari irin wanda ka tsara wa rayuwarka. Ka zamanto mai hakuri, dauriya bin ka’ida, tsari da jajircewa akan manufarka.

  Mai karatu na iya duba: Abubuwan dake durkushe baiwa da basirar yara

  Ta yaya zaka tsara kundin rayuwarka? Wannan abu ne mai sauki. Abu na farko shine yi kokarin sanin ko kai waye? Kai waye ba yana nufin menene sunanka? Suwaye mahaifanka? Kai dan wace kasace ko gari ba?

  Kai waye na nufin, wani irin baiwa ke tattare gareka? Anan, mutane dayawa na karancin fadada tunaninsu kan kalmar nan ta baiwa. Wasu sun dauki kalmar baiwa a matsayin ‘daukaka’ ko ‘yin ficce’ nan take, wanda lamarin bahaka yake ba.

  Ya kamata a sani, ita baiwa mataki mataki ce. Ina nufin a kowani yanayi na rayuwar al’umma, cikin wadata ko rashin wadata, Allah kan yi wa bawansa baiwa. Wani  baiwarsa ta kere-kere ne, wani zane, wata lalle, wani/ta saka, wani kirkirar labari, wani iya magana, wani sassaka dadai sauran su.

  A cikin ire-iren wadannan da makamantansu, idan kana iya yin daya daga ciki, wanda idan a kace wani ya yi bazai iya ba. Iyawarka shi ne baiwa.

  Don haka a yayin da ka fahinci irin muhallin baiwan da Allah ya yi maka, mataki na gaba shine, me dame kake tunanin zaka yi don ka fadada shi? Anan bai kamata ka tsayar da tunaninka a iya makwabta ko ‘yan unguwarku ko garinku kawaiba ba. Alal misali, idan baiwarka ta sakar taburmace, abin da ya dace ka fara tunani shine wani irin sabon salon taburma zaka saka? Wace iri ce a iya tunaninka ba’a taba saka irinta ba? Kuma ta burge mutane ba ‘yan kasuwar garinku kawai ba? Bayan haka, wani irin abu ne da al’umma ke amfani da shi wanda idan ka kirkiro ta hanyar saka zai saukake rayuwar al’umma? Yaya kuma za ka yi ka tallata su?

  Ayayin da ka sami ire-iren wadannan tunanin, da tambayoyi, da ra’ayoyi daban-daban, za su sauko maka a duniyar kwakwalwarka. Awannan lokaci ne zaka baiwa kanka-da-kanka amsar cewa ba abu ne da zaka yi shi arana daya ba.

  Abin da ya kamata ka yi shine, TSARA KUNDIN RAYUWA akan irin turbar da ka ke bukatar duniya su gani su kuma sanka akai. Anan akwai bukatar sanin, ta yaya za ka fara inganta aikin? Wani irin salo zaka shigo da shi cikin sakan? Me za ka kirkiro ka shigo dashi ya zama sabo a duniyar saka? Me da me kake bukata? Wani irin kalubale kake tunanin iya fuskanta? Ta yaya zaka iya warware kalubalen? Wace irin rayuwa ta dace ka gudanar? Kana bukatar neman ilimi ko karin karatu? Wace irin .macce kake bukata a rayuwarka? Yaya kake bukatar tsarin rayuwar iyalanka ta kasance?

  Yayin da ka cimma nasarar yin iri wadannan tambayoyi da kuma samun amsoshin su, sai ka gina su a matakan tafiyartar da rayuwarka. Abu mafi muhimmi shine, ka yi iya kokarinka wajen aiwatar da su daidai da yanda ka tsara.

  Aikata hakan shi ake kira HANGEN NESA da TSARA KUNDIN RAYUWA.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

 • Kin yi ta saurare ki ji ya turo manyansa zuwa gidanku amma har yanzu shiru: Ga dalilai

  Posted Jun 29

  Mata mu kan fada cikin yanayi na yaudara cikin sauri ba tare da mun farga ba. Musamman idan namiji ya zo da batun auren ki zan yi, mu kan mika duk wata ragamar rayuwar mu a gare shi, muna masu amanna da mika wuya dari bisa dari.  Sam bama hangen da mi yazo a lokac...

 • Manya-manyan kura-kurai da ma'aurata ke yi ba su sani ba

  Posted Jun 27

  Aure na iya zama abu mafi kololuwar jin dadi da walwala a rayuwar dan Adam, a wasu lokuttan kuma ya kan zama tamkar mutum na zaune a gidan yari ne wani sa'ilin ma na gidan yari yafi ka kwanciyar hankali. Hakan duk ya ta'allaka ne da waye ka aura.  A wannan zamani ...

 • Ciwon kan migraine: Dalilai da alamun kamuwa da shi da kuma hanyoyin magance shi

  Posted Jun 26

  Ciwon kan da ake kira da migraine, cikin harshen Turanci, wani ciwon kai ne mai tsaninin gaske da ke kawo rashin jin dadi kamar su tashin zuciya da kuma jiri. Wannan kalma ta migraine ta samo asali ne daga harshen Faransanci wato daga kalmar ‘megrim’ wadda m...

 • Alamomi goma dake nuna cewa soyayya ta kare tsakanin ki da shi

  Posted Jun 22

  Akwai bambanci tsakanin namiji na sonki da kuma bai sonki, wanda zai nuna hakan a aikace, a baki da kuma yanayin mu'amalar ki da shi.  Da yawan mata za su fara tunanin ko nayi wani laifi ne? Miye dalilin canzawar shi? Mi ya kamata na yi wajen kara karkato da hanka...

View All