Makalu

Ingancin rayuwarka/ki shine amfani da dama da lokaci

 • Shin ko ka taba tambayar kanka-da-kanka me ake nufi da amfani da lokaci? Ka kuma taba kokarin ka fahintar da kanka cewa ba ko da yaushe ne dama ke nanata kanta ba? Ka kuma taba sanin cewa dama da lokaci tamkar danjuma ne da danjumai?

  Akwai bukatar mu dada fahimtar cewa, ita kanta duniya tana tafiyane akan lokaci, yayin da halittun cikinta ke rayuwa bisa dama da lokacin. Akwai abubuwa daban-daban da muke son yi a rayuwarmu ta duniya yayin da bisa sakaci, ganganci ko iko irin na Ubangiji lokaci ya wuce. Kuma duk karfin ikonka, mulki, sarauta dukiya ko fakirancinka baza ka iya dawo da lokaci don ka yi amfani da shi yanda ya dace da burinka ba. Hakan na nufin, baza ka iya dawo da jiya yau, ka mayar da yau gobe ba.

  Sabo da haka, akwai bukatar mu kasance masu amfani da kundin tsarin rayuwar mu akan lokaci, mu kuma yi amfani da dama dake tattare a cikin lokuta; ta haka ne zamu samu kofar tallatawa duniya dinbin baiwa da basira da ubangiji ya halitta ya sutura mana a cikin kwakwalwarmu.

  Yin amfani da dama akan lokaci shi zai haifar mana da habaka tunaninmu da kara mana basira akan baiwarmu.

  Idan kai ango ne sabon aure, yi amfani da wannan damar wajen tsara rayuwar zamantakewar ku tun kafin tafiya ta yi nisa, dama kuma ta kaurace maka. Ta hakane iyalanka za su ginu akan turba mai kyau mai kuma tsari da ka’ida.

  Idan kuma Allah ya baka haihuwa, yi amfani da matsayinka na mahaifi ka kuma yi aiki da dama da lokaci wajen tarbiyartar da ‘ya’yanka a tafarki mai kyau. Sabanin haka, za a wayi gari ‘ya’yanka su fi karfin umurninka don kuwa kabar dama a baya.

  Ya ku ‘yan uwana matasa, babu abin da yafi neman ilimi akan lokaci dadi. Idan ka yi amfani da damar da ka samu wajen neman ilimi, haka ka yi amfani da lokaci wajen yin karatun zaka fahinci cewa awannan lokaci ne kwakwalwarka ke da kishin ruwan neman ilimin, haka baiwa da basirarka (wadanda kaima baka sani ba) ke kokarin tunkudowa waje don duniya su sani.

  Hakan yake a lokacin neman aiki ko sana’ar yi. Matasa da suka kammala karatunsu na jami’a ko kwaleji kan tura kansu zaman banza; a dalilin rashin sanin muhimmanci lokaci. A yayin da ka ginu a kan zaman banza, sai a wayi gari ka tsinci kanka cikin shaye-shaye, sata ko rayuwa a gidan rawa.

  Sannan za a iya duba: Inda maita ke amfani a rayuwar al'umma

  Faruwan hakan na nufin, banzan rayuwa da ka tsinci kanka a ciki ne yayi amfani da dama da lokaci akanka. A maimako kai ka yi amfani da wannan dama da lokaci yanda ya dace.

  Idan muka sake duba al’amari ta wani bangare, misali, akan wayi gari wasu masana’antu su tallata hajarsu na neman  ma’aikata, sau dayawa sukan fitar da ka’idodi wanda daya daga ciki shine shekaru. Abin nufi sukan kaiyade iya adadin shekaru mutumin da suke son dauka aiki. Wannan na nufin, matukar shekarunka sun wuce ka’idar da suke bukata, duk iliminka dama ta wuce ka.

  Haka idan muka kalli al’amari a gefen aure ko neman aure. Matukar baka yi amfani da lokaci da damarka tun kana kan lokacinka ba, za ka iya fuskntar kalubale iri-iri wajen neman aure. Ya Allah mace da kai ka ke so, tace shekarunka sun mata yawa. ko iyayenta suce baza su iya ba sa’an mahaifinta ‘yarsu ba.

  Idan muka tattatara akalar tunaninmu ya zuwa maganar lahira, zamu iya fahimta cewa kowani mai rai yana jiran lokacin mutuwarsa ne. Kuma duk abin da ka ke bautawa, dole akwai ka’idodin da lokacin yi masa bauta. Yayin da ka yi sakaci waje amfani da lokutan da suka dace, kai kanka za ka sani cewa akwai damuwa matukar ka mutu ka sadu da ubangijin naka.

  Don haka, mu kasance masu amfani da lokaci a yanda ya dace, a yayin da ya dace, a kuma cikin lokaci da ya dace. Mai karatu na iya karanta wannan makala: Salallan mazan banza don hadaka da matan banza da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All