Makalu

Macce ‘yar wuta cikin matan aure

 • Ko kasan wa ake kira matan auren? Matar aure itace wacce ta dauki amanar mijinta da duk wani hakki na aure da Allah ya dora wa macce, kuma ta yi alkawarin kare shi. Ko kunsan bakar shafin rayuwa da wasu matan aure ke gina rayuwar aurensu a ciki? Galibin matan aure ayau sun dauki aure tamkar wani mayafi ne da kawai zai lullube duk wani aikin ashsha da suke yi. Matan aure dayawa sun maida zina tamkar ado. Allah ya tsare.

  Matan aure da suka yi kaurin suna wajen zina sun dauki wannan mummunar hanya ne don kariya guda uku:

  1. Suna da lasisin mallaka wa mazjensu cikin shege da suka samo shi a waje
  2. Suna da kariya da baza a yi saurin zarginsu da aikata zina ba
  3. Suna kuma da kofar samun kudi cikin sauki

  Siffofin matan aure mazinata sun hada da

  • Musu da jajircewa akan karya
  • Amfani da dukiyarta ko namijinta wajen jan hankalin wani namiji
  • Yawaita fita
  • Tallata kanta ta hanyar shiga mai jan hankalin maza
  • Walwala cikin kudi\sutura sabanin gwargwadon samunta da namijinta

  Matan aure da ke aikata zina na amfani da wasu hanyoyi kamar haka:

  • Yawan neman izinin zuwa unguwa
  • Yawan karyan aiki ya yi yawa a wajen aiki
  • Yin sana’ar saya da sayarwa da yawan tafiye-tafiye wajen
  • Amfani da bukin kawaye ko ‘yan uwa
  • Yawan son ziyartar ‘yan uwa a wani gari

  Wani abin bakin ciki shine, wannan mummunar rayuwa a cikin mata na faruwa ne a kowani irin mataki na rayuwar macce. A karamin mataki na talaka, wasu matan kan bar gidajen mazajensu da sunan zuwa unguwa sai su tafi gidan karuwai ana zina dasu a na biyan su kudi. Kamar yadda ya taba faruwa a Kano shekaru da suka gabata. ‘Yan Hisba sun taba kai samame a gidan karuwai inda suka kama mata wadanda biyu daga cikinsu matan aure ne.

  Abangaren matan manyan ‘yan kasuwa kuma, sukan yi harkar kasuwancinsu zuwa Dubai da sauran kasashen Duniya.  Asau tari da yawa daga cikin tafiye-tafiyen nasu na da alaka da yin masha’a da manyan gwannati.

  Haka yake idan muka kalli abin abangaren masu mulki. matan aure kan yi masha’ansu ne da direbansu ko direban mai gidansu ko kuma wanda mai gida ya yarda da shi. Anan matan kan yi amfani da hikimomi daban-daban. Idan mai kurucciyar shekaruce, takan yin amfani da hikimar nuna soyayya, idan kuma  tana da shekaru takan yi amfani da kudi. Hakan idan mai iko da mijinta ce takan yi amfani da barazana daban-daban ga wanda take son su yi masha'ar.

  Mu sani mutuwa gaskiya ce haka ma isabi! Mai karatu na iya duba: Salallan mazan banza don hadaka da matan banza da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All