Makalu

Abubuwan dake durkushe baiwa da basirar yara

 • Idan muka dubi kasashen Duniya da suka ci gaba, rayuwanrsu ta samo a saline daga taimakekeniya dake wanzuwa a tsaninsu. Masu baiwa da basira a cikinsu kan samu tallafi na shawarwari, kwarin gwaiwa, Karin ilimi, kudin ko kayan aiki.

  Idan muka, dawo sauran kasashen duniya kuma, muasamman kasata Nijeriya, ba a kallon baiwa ko basira a matsayin wani abin da zai kawo cigaba a cikin al’umma balle kasa baki daya.

  Hakan shi ya taimaka wajen janyo durkushewan duk wani da Allah ya yi wa baiwa da basira a kasata Najeriya. Hanyoyi da kasata ke  bi wajen dakulewar ire-iren wadannna mutane sun hada da:

  1.Mugunta da aiki da sihiri: kodayake, wasu al’umma basa kallon sihiri a matsayin wani abu da ke taka rawar gani wajen murkushe rayuwan masu basira, amma gaskiyar magana ita ce, sihiri gaskiya ce kuma wasu mutanen masu mugunta suna amfani da ita. Duk wani mugu yasan abu mai muhimmanci, don haka, sukan iya gane yaron da ya tashi ko aka haife shi da baiwa ko basira. Tsananin mugunta da suke da shi a zukatansu, kan basu damar yin shege-shege na sihiri don durkushe  kyauta da Allah ya masa.

  2. Karancin tallafi: wasu shugabanni a  a yau, al’ummarsu basa cikin tunaninsu. Don haka, basu da lokacin nazari ko mu’amala cikin jama’a balle su san irin tallafi da zasu basu. Wasu kuma, basa kaunar ganin wani ya daukaka idan ba su ba. A bisa wannan dalili, basa iya mika tallafinsu ga masu baiwa da basira.

  3. Rashin goyon baya daga iyaye: wasu yaran sun tashi da kirkire-kirkire tun suna wasan kasa. Sukan kirkiri motan kwali ko ta kara. Yaron da ke da basira akai, zai kasance yana girma amma ba a raba shi da yin ire-iren wadannan sa'i da lokaci. Anan, wasu iyayen  yaran kan kalli faruwan hakan a matsayin kwarewa wajen wasan banza, ba tare da dubi kan madogaran hakan ga shi yaro ba. Daga karshe, iyaye kan sa yaransu a gaba da duka sai idan sun daina. Anan, baiwa da basirarsa ke durkushewa.

  4. Rashin dora yaro akan tubali da ya dace: a wani bangare kuma, koda a ce iyaye sun fahimci irin baiwar da ‘ya’yansu ke dashi, su kan bi ra’ayin zuciyarsu ne kawai. A bin nufi, sukan tilasta ‘ya’yansu wajen karanta abin da basa sha'awa. Dalilin kawai, don dan makwabtasu likitane ko injiniya.

  5. Rashin kayan aiki: Duk yanda yaro ya so ya baiyana baiwarsa da yanda iyaye suka so dansu ya bayyana baiwarsan, ba zai yiwu ba matukar ba kudi ko kayan aiki dake gareshi.

  Ya zama dole shugabanni, iyaye da sauran al’umma su kasance masu tausayi da yin halin yakamata don ci gaban al’umma da kasa baki daya.

  Mai karatu na iya duba: Malamai a cikin kunci akwai abin dubawa da sauransu

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Wai shin mene ne data da kamfanonin layukan waya ke sayar mana?

  Posted Oct 13

  Kamar wata biyu da su ka wuce, Mallam Rabiu Biyora ya yi tambaya akan DATA da mu ke saye daga kamfunan waya inda ya ke cewa "DATA da kamfanonin layukan waya ke siyar mana, har muke amfani da ita wajen hawa Internet, su kamfanonin siyowa suke daga kasuwar siyar...

 • Egg and vegetable pocket

  Posted Oct 9

  A yau makalarmu ta girke-grken zamani zat yi bayani ne akan yadda ake hada wani abincin zamani mai suna egg and vegetable pocket. Ga yadda ake yin sa kamar haka: Abubuwan hadawa Filawa kofi biyu (flour 2cups) Baking powder 1½tsp (karamin cokali) Butter coka...

 • Rayuwar zamani: Babi na biyu

  Posted Oct 6

  Dedicated to Autan Hikima. Raihan na komawa office ya aiki masinga akan yaje yace ma head din ko wani department yana son ganinsa aconference hall, babu 6ata lokaci duk yabi ya fadamusu kafin ya koma ya sanar da zuwansu. Yana zaune a office kafin ya fara komai yaga ho...

 • Yadda ake hada sausages sultan chips

  Posted Oct 6

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirinmu na Bakandamiya. A yau Insha Allahu zamu yi bayanin yadda za ki hada sausages sultan chips. Abubuwan hadawa Dankali (irish) Sausages Carrots Albasa Tattasai da tarugu Man gyada Green peas Green pepper M...

 • Rayuwar zamani: Babi na daya

  Posted Oct 4

  Sulaiman bai yi mamakin ganinta ahakan ba domin hakan dabiar tace. taku take cikin isa da gadara irinta 'ya'yan masu kud'i y'a'yan masu hannu da shuni, Muhievert kenan yarinya fara doguwa kyakyawa, gata da k'ira mai kyau tsaruwarta ya zarce duk inda mutun ke tunani. Aka...

View All