Makalu

Inda maita ke amfani a rayuwar al'umma

 • Akwai daurewan kai ga wasu mutane a duk lokacin da aka ce MAITA. Wasu kan kasa gaskanta cewa MAITA na daga cikin buyayyun baiwa da Allah yayi wa bayinsa. Amfani da shi kuma, ya danganta da halin shi bawa da Allah ya masa baiwan. Wasu ta kyakykyawan hanya, wasu kuma ta munanan hanya suke amfani da shi.

  Idan muka leka kasashen duniya da suka yi fintinkau fagen cigaba, MAITA na daya daga cikin hanya da suke sarrafa cigabansu. Mu yi dubi da abubuwan saukakewa da tausasa jin dadin rayuwa. Mu yi dubi da ire-iren motoci da muke hawa a yau. Mu sake kallon tsarin gidajen bene da muke kwana. Hakama na’urorin na tsaro da muke sawa a cikin gidajenmu.

  Sakamakon duniyar kimiyya da muke ciki, samun sababbbin abokai da sada zumunci da wani a ko’ina yake ko take a fadin duniya na faruwa a cikin kankanin lokaci. Mutane da yawa a kasashe daban-daban na fadin duniya, suna sarrafa MAITA ta kyakykyawar hanya domin yin kere-kere da samar da magunguna na cututtuka daban-daban dake addaban duniya. Rayuwa ta saukaka, abubuwan ban mamaki da suka samu asali daga kere-kere sun yawaita. Alal misali:

  1. Muyi dubi da rawar gani da wayar salula ke takawa. A yau an wayi gari, masu sarrafa MAITA aduniyar kimiya sun fadada ta ta yanda idan kana magana da mutun ko’ina yake a fadin duniya, zaka ganshi zai kuma ganka matukar kana aiki da irin  wayar.
  2. Mu yi dubi da yanda na’ura mai kwakwallwa ke iya amsa tambaya a cikin kankanin lokaci.
  3. Yi nazari sosai kan yanda jirgin sama ke diban daruruwan mutane ya tashi sama. Ayau ‘yan kimiyya sun kera jirgin da ke sarrafa kansa da kansa ba tare da aiki da matuki ba.
  4. Mu kuma yi dubi da yanda turawa ke shiga karkashin teku su yi kwanaki daga karshe su fito su gina gada akan tekun mai ban al’ajabi.

  Amma idan muka dawo kasata Najeriya, mutane dake dauke da wanna MAITA, yanda suke sarrafata ya sha bamban da saura ‘yan uwansu dake kasashen duniya. A kasata Najeriya ne kawai uwa ke amfani da maita wajen cinye danta, ko jikanta, kanwarta ko wani nata. Haka shi namiji kan yi amfani da maitan wajen mulkin danniya ko dakile rayuwan kasuwancin dankasuwa, dukiyar mai dukiya, fahimtar mai fahimta, hankali mai hankali, cigaban mai cigaba ko haukata mai hankali; ta hanyan tsafi da amfani da sihirin maitan.

  Ya ku al’umma, mu sani cewa, cigaba baya faruwa matukar zamu kasance masu amfani da baiwa ko kyauta da Ubangiji ya mana ta miyagun hanyoyi. Yana da kyau muyi koyi da kasashen da suka cigaba a duniya. Sannan mai karatu na iya duba: Salallan mazan banza don hadaka da matan banza da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All