Makalu

Salallan mazan banza don hadaka da matan banza

 • Sakon mu na yau, mazan banza na nufin mazan dake da matansu a gida amma cikin kwanciyar hankali suna masha’arsu da matan banza a waje. Ire-iren wadannan maza suna aiki ne da hikima da basira da ilimi da salalla daban daban wajen zaluntar matarsu da isar da sakon aikata sabonsu ga Ubangiji. Wasu daga cikin ire-iren wannan salallan, duk karfi tunanin da basirar mace baza ta gane ba.

  Wadannan salalla sun hada da:

  Harka da mace mai fuskar kamila

  Akwai halittan wasu mata in an kalli su suna da fuska irin ta kamun kai,alkunya,  kamilanci da tsoron Allah, don haka fuskarsu bata da alaka da duk wani aikin na masha’a. saidai, wasu daga cikin ire-irensu, shedanune hasalima suna amfani da irin wannan fuska tasu su rinka aikata abin da ba a zato daga garesu. So dayawa, akan sami iren su zaune da matar aure, ya Allah kanwarta, ‘yar makwabtarsu, ‘yar uwarta ko ‘yar uwan mijinta.

  Munafukin mai gida kan gane ire-iren wadannan matane daga ‘kallo’. Su kuma matan kan gano irin wadannan maza daga ‘cinfidar fuska, ma’ana, fuskarsa kan rubuta mata muradinsa. Anan akan sati lokaci don musayan lamba ko adireshi, idan kuma a gida daya ake Magana ta kare’ wai mata ta ce wa mijinta maye.

  Mallakan buyyayyun gidaje

  Wasu magidanta musamman masu hali da shuni, sukan sayi gida na musamman a wasu unguwanni da baza azaci ire-irensu da mallaka ba. Wasu kuma sukan yi gidan gona a wasu kauyuka. Anan suke masha’a da zinace-zinace da matan banza. Lokutan aikata wadannan danyen aiki sukan jerantasu cikin lokutan zuwa aiki ta yanda matansu zasu saba da kuma yin imanin cewa mijinsu na wajen aiki ko kasuwa.

  Harka da matan aure

  Kamar da ake samun mazan aure na banza, haka ake samun matan aure na banza. Don haka, zinace-zinace wasu mazan aure idan ya rika yakan yi kicibis da matan aure dake da akida irin nasu. Wasu mazan na da ‘yan kawali masu nemo masu iren wadannan mata. Yana da wahala a iya gane barna da suke shukawa don mace kan kai cikin ‘ya’yan wani ga gidan mijinta, shi kuma na yada na shi barin jikin a wasu gidajen.

  Hutun karshen mako/tafiya don kasuwanci

  Wasu mazan kan dowa da tsaraba na musamman a matsayin sun yi tafiya, alhali suna gari daya da matansu. Kawai suna masha’arsu ne da matan baza da sunan sun yi tafiya.

  Musani, duk abin da ka yi sai an maka, azabar kabari na nan na jira! Mai karatu na iya duba: Macce 'yar wuta cikin matan aure

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Tue at 10:07 AM

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

 • Yawaitar binciken wayar miji: Dacewa ko rashin dacewa?

  Posted Jul 31

  A wannan zamani matsalolin da suke cikin aure musamman anan Arewacin Najeriya abin ba a cewa komai idan muka lura da ire-iren labarai da suke yawo yau da kullum a kafofin sada zumunta, wato social media. Duk lokacin da ka shiga social media idan yau baka ga labarin wata...

 • Takaitaccen bayani game da gravitational field

  Posted Jul 27

  A physics, gravitational field model ne da ake amfani da shi wajan bayanin tasirin da massive body ya ke da shi wajan zuwa sararin samaniya around itself producing a force on another body. Gravitational force of attraction da ke tsakanin body guda biyu ana governing din...

 • Sakamakon bincike game da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi a Najeriya

  Posted Jul 24

  Matsalar shaye-shayen miyagun gwayoyi matsala ce da kusan kowa da kowa na iya tabbarwa akwai shi a cikin al’umma musamman mu a Najeriya. Idan wani baya sha a gidanku, ko cikin danginku to kuwa lallai ba za a rasa masu yi ba a unguwarku ba. To amma duk da haka a ku...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Jul 6

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuw ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a n...

View All