Makalu

Sirrantattun matsaloli dake kawo cikas a shimfidar aure

 • Idan aka dauke bayyanannun matsaloli, kama daga aikace-aikacen gida, hidimomi ilimi da sauransu, akwai wasu boyayyun  (sanannun ga mata da miji) halaye dake kawo matsaloli, wani zubin ya kai ga mutuwar aure. Su wadannan matsaloli miji kan ji nauyi ko kunyar bayyanasu ga surkunayensa musamman a kasashe ko garuruwan da alkunya ke tasiri cikin al’adunsu. Hakama ita mata kan ji nauyi bayyanasu ga nata surkunayen ko iyayenta.

  Wadannan sirrantattun matsaloli sun hada da:

  • Wasu daga cikin maza, yayin da suka tashi kusantar iyalansu, sha’awa dake garesu itace kawai bukatarsu. Don haka, sukan kalli mace tamkar wata godiya da ba sai an lallabata ba. Lalabawa anan na nufin kirkirar hanyoyin da itama zata samu sha’awarka, yanda bukatarka da nata zai biya ba tare da ka biya bukata ka barta cikin bacin rai ba. Ire-iren wadannan dabi’un kan sa macce ta gina wani shafi  dauke da karancin kima azuciyarta. Za a waye gari sha’awar da takan yi kan mijinta ya fara dishewa. Akwana a tashi, idan shaidan yayi dace karon batta da ire-irensu sai ya fara sa masu sha’awar wani ko wasu mazaje da suke gani ko suke jin labari. Anan ne za a waye gari mai gadin gidanka shima mijin matarka ne.
  • Rashin sakewa, wasu mazajen yayin hadaka da matarsu, sukan bayyana masu wasu halaye kamar, gadara, iko, umurni, daure fuska da rashin kallon matarsu a matsayi wata abace mai muhimmanci. Babu shakka, wanna cinfuska ne dake kona zukatan mata. Yin hakan, kan sa mace tunani daban-daban kan halin mijinta. Zata fara zargin sa da ko yana neme-nemen mata a waje. Matsalar ba a nan ma ta tsaya kawai ba, babban abin takaici da macce ke tsintar kanta a ciki shine, duk yanda takai ga biya wa mijinta bukata bazata gani a fuskarsa ba belle taji daga fatar bakinsa.

  Idan mata da miji sun dau lokaci cikin wanna yanayin rayuwa, zama kan tsananta daga karshe komai na iya faruwa. Don haka mu farga.

  • Rashin tsafta: rashin safta ba daga mace kawai yake faruwa ba. Daga cikin maza, a kwai wadanda idan suka wuce gefenka zaka ji tamkar ka yi amai, ballantana ace kun hada daki guda. Mata da yawa suna fama da irin wadannan tashin tashana na doyin dutti. Abin takaici shine, maza dake da irin wannan karancin tsafta sun kasance masu iko, izza da zafin rai ga matansu.

  A karshe, ire-iren wadannan halaye kan raba zaman mata da miji. Sannan mai karatu na iya duba: Salallan mazan banza don hadaka da matan banza

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted 2 hours ago

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All