Makalu

Malamai a cikin kunci? Akwai abin dubawa

 • Ilimi dai shine fitila mai tsarkake rayuwar al’umma baki daya. A tsarki da tsarkake ayyuka, babu addinin da baya bukatan ilimi don gudanar da aikin ibada a cikinsa.

  Hakan na nufin, babu yanda al’umma zasu rayu cikin seti batare da samun maluma a cikinsu ba. Malami mutun ne mai yin tsuwar daka wajen ganin yayi bincike kan abinda yake bukatar ilimintar da al’umma. Muradinsa a kullun shine tabbatar da bada ingantaccen ilimi na zamani ko na addini. Sakamakon aikin malami a cikin al’umma ne ya haifar da samun manyan shaihunai, daktoci, furofesosi, masu aikin damara da sauran kananan maluma. Bugu da kari, hanun aikin malami bai tsaya a nan kawai ba, karfin hidimar aikin malami yayi gudumawa gaya wajen shinfida tsarin zaman takewa a cikin al’umma, mussamman tsarin mulki wato shugabanci. Aikin ilimin malami ya kenkeshe tsarin mulki daga masinja zuwa shugaban kasa, a kowani mataki na matsayi kuma na da irin martaba da ake bashi.

  Idan muka yi dubi akan ciyaman, gwanna da ministoci, karfin kima, martaba da daukaka da aka basu, yakai matakin da ake hadasu da jami’an tsaro. Motoci da suke hawa kuwa sun fice gaban kwatance. A nan, wani abin da rayuwa ke mantawa shine, kama daga masinja zuwa shugaban kasa duk “almajiran malam ne”.

  To amma, abin kunci, bakin ciki da takaici shine, mafi wayan kasashen duniya musamman Afirka, ba wanda al’umma ke kallo wahalalle, walakantacce, talaka matsiyaci kamar malami. Idan muka kalli bangare malaman addini, sutura mai kyau da suke sawa mafi yawanci na samu asaline daga kwance da masu kudi ke yi musu. A gefen aure kuwa, asodayawa mace sai ta lalace ko anga zata lalace ake ba malamin addini sadaka. Don hakanema idan aka zo mata budan kai sai a sa mata suna “ta annabi”.

  Ga malamin boko kuwa, musamman a kasata Najeriya kuma jahata Taraba, neman kashin kifi a ruwa yafi malami saukin samu fiye da neman bashin kudi ko na abinci. Idan muka zunduma duniyar neman aure ga malamin, ‘yan mata a yau sun yi wa manemensu lakabi da suna ‘alpher’. Budurwa kan tambayi kawarta maneminta a alpher nawa yake? Don kuwa alpher A= na nufin Accountant, B=Banker C=Custom D=Director E=Excellency F=Finance minister G=Governor H=Honorable. Atakaice idan ka fada alpher T=(Teacher), aiki ya sameka don  idan ba tsananin rabo ba, neman aurenta ya wuce ka.

  Abin zubar da hawaye shine, wadan da suka ja ragamar zubar da kiman maluma sune ‘almajiran malam’ musamman wadanda ke juya karagar mulki yanda suke so.

  Ya al’umma, mu dubi girman Allah mu zama masu fidda malumanmu daga cikin kunci da takaici na rayuwa. Wannan ke nan, mai karatu na iya duba: Abubuwan dake durkushe baiwa da basirar yara da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All