Makalu

Matsalolin jami'an tsaro: Laifin kasa ko na su jami'an?

 • A duniyar ilimi, a duniyar tausayi da duniyar da gwannati tasan makamashin aikinta, jami’an tsaro mutane ne da suka kware kan aikin su, suna da hikima wajen bincike, suna da baiwa da basira wajen kama mai laifi. Bugu da kari, mu’amalarsu da al’ummar kasarsu na taimakawa wajen kau da barna da ta’addanci. Talakawa basa shakka ko fargaban kai kukansu gaban jami’in tsaro komin girman ofishinsa.

  Saidai duk da haka, rayuwa bata yi kasa a gwaiwa ba wajen bayyana gurbatattun jami’an tsaro, wadanda duk lokacin da talaka ya gansu ya sani cewa asara ta zo masa, don talaka na iya zama mai laifi alhali bai ji-ba- bai-gani ba.

  Ire-iren wadannna jami’an tsaro sukan yi:

  • aiki ne don kansu ba don Allah ba
  • su kan yi kamen dare ba don laifi ba, sai don samun cin hanci da rashawa.
  • su kan kama mata ba don sun yi laifi ba, sai don su yi lalata da su.
  • su kan yi gaggawan kai dauki ba don taimako ba, sai don su sati kudi wadan suka mutu.
  • su kan harbe mutun har lahira ba don yayi laifi ba, sai don ya ga mugun aikinsu.
  • su kan tura mutun gidan maza ba don yayi laifi ba, sai don ya nuna masu yasan ‘yancinsa.
  • su kan yi wa mutun sharri ba don yayi laifi ba, sai don ya tsaya akan gaski.

  Babban abin bakin ciki shine, sau da dama gurbatacciyar gwannati kan taka rawar gani wajen faruwan ire-iren wadannan zalunci. Don kuwa gurbatacciyar gwamnati kan yi amfani da miyagun jamai’an tsaro don kau da wadan da bata son gani a doron kasa.

  Akasari irin wadannan gwamnatocin kuwa basa iya biyansu salari akan lokaci don su tagayyarar da jami'an tsaron ko don su yi abinda suke so. Basa samun muhalli da ya kamata. Basa iya fadar matsalarsu sai dai su bi umarni kawai. Idan an masu canjin wurin aiki zuwa wata jaha, ba’a damu da suna da kudin mota ba belle na abinci. Duk kayayyakin aiki - kama daga yuniform zuwa batirin tocinsu - irin wadannan gwamnatoci bata damu su tabbatar sun wadata dasu ba.

  Akwai bukatar gwannatin kasa ta kasance mai duba rayuwar jami’an tsaron kasarta da idon tausayi, basira da rahama. Ta zama mai sauke duk wani hakki dake kanta, domin kuwa, kyawawan aikin jami’an tsaro ne ke sa kasa ta yi bacci da minshari ba tare da fargaba ba.

  Sannan mai karatu na iya karanta: Alamomin shugaba na gari da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted Sat at 3:40 PM

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All