Makalu

Farfesun kan rago

 • Abubuwan hadawa

  1. Kan rago
  2. Attarugu 5
  3. Albasa 2
  4. Maggi
  5. Gishiri
  6. Kayan kamshi
  7. Tafarnuwa 3

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki wanke kan ragon, ki gyarashi sosai sai ki zuba a tukunyarki, ki yanka albasarki ki sa a ciki, ki sa maggi da gishiri kadan, anan sai ki zuba ruwa sosai, sai ki rufe, ki dora a wuta. 
  2. Ki barshi ya nuna sosai, sai ki jajjaga attarugu da albasa da tafarnuwa ki zuba, sannan ki sa kayan kamshi. Ki sake rufewa ki barshi ya ci gaba da dahuwa.
  3. Idan ya yi za ki ji gida ya dau kamshi, sai ki sauke ki zubawa maigida da yara aci da safe. Ki na iya hadawa hadawa da biredi ko doya.

  Sai mun hadu a girki na gaba. Na gode. Sannan za a iya duba: Lemun abarba da madara da lemun kankana da sauransu.

  Hakkin Mallakar Hoto (Photo Credit): Afrolems

   

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

  Posted Wed at 8:34 PM

  Alfanun tsiro ko ganye a matsayin abinci ko hanya ta samar da waraka (magani) daga wasu nau’o’in cututtuka ga ɗan Adam daɗɗaɗe abu ne a tarihi. Don haka, kusan kowace al’umma ta tanadar da hanyoyin sarrafa nau’ukan abincinta da kuma samar da kari...

 • Bayanai game da Boyle's Law

  Posted Mon at 7:09 PM

  Boyle’s law yana daya daga cikin laws na gas wanda a makala ta da ta gabata na yi bayani akai. Kamar yadda na fada a baya, a yau kuma zamu je kai tsaye ne don duba daya daga cikin gas laws. Wannan law din shine boyle’s law. Wani lokaci akan kira bo...

 • Abubuwan da dalibanmu ya kamata su sani kafin rubuta JAMB, WAEC da NECO

  Posted Apr 12

  A yau za mu ci gaba ne da tattaunawarmu akan jarabawar JAMB da muka faro a baya. Idan mai karatu na bukatar sanin abinda muka yi a baya zai iya duba inda muka tattauna akan Ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta game da jarabawar JAMB. Insha Allah za mu ci gab...

 • Hanyoyi biyar (5) da za a bi don rage damuwa (anxiety)

  Posted Apr 10

  Zamu iya cewa duk wani dan adam da Allah ya hallita a doron kasa yana da wani abinda ya ke tsoro. Wannan tsoro kuwa shine akasarin lokaci ke jawo abinnan da ake kira a Turance da anxiety attack (damuwa mai tsanani) ko kuma panic attack. Anxiety ko damuwa mai tsanani wan...

 • Yadda ake hada apple smoothie

  Posted Apr 8

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada apple smoothie. Abubuwan hadawa Apple (tufa) Sugar ...

View All