Makalu

Dambun masara

 • Abubuwan hadawa

  1. Tsakin Masara
  2. Zogale
  3. Attarugu
  4. Albasa
  5. Man gyada
  6. Dakakkiyar gyada
  7. Maggi
  8. Kayan kanshi
  9. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke tsakin masaranki ya fita tas, sai ki tsameshi a mararaki.
  2. Idan ya tsane sai ki zuba ruwa a tukunya mai dan zurfi,anan sai ki sa marfi wanda zai rufe iya kan ruwan.
  3. Sai ki dauko buhunki mai kyau ki zuba wannan tsakin, sannan ki sa a cikin tukunyarki, ki rufe ya turara.
  4. Idan ya turara sai ki fito dashi ki juye a roba mai kyau, ki jajjaga attarugu ki zuba sai ki yanka albasa ki sa a ciki, ki sa maggi, da gishiri, da kayan kanshi, da gyada, da zogale, ki juyasu sosai.
  5. Sai ki mayar cikin buhunki ki sa tukunya ya turara kamar minti ashirin, idan ya yi za ki ji yana kamshi.
  6. Sai ki bude idan ya yi sai ki sauke, ki zubawa maigida da yara, ki sa man gyada da yaji.

  Na gode sosai. Sai mun sake haduwa a girki na gaba. Sannan ana iya duba: Suyan dankali mai nama da kwai na musamman da kuma lemun mangwaro da sauransu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): arewacafeteria

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All