Makalu

Dahuwar shinkafa da wake  

 • Asssalamu alaikum wa rahmatullah ‘yanuwa. Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. A yau zamu koyi yadda ake dahuwar shinkafa da wake. In kun shirya, ga shi kamar haka:

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa kofi 1
  2. Wake kofi 1
  3. Man gyada
  4. Yajin Barkono
  5. Salat
  6. Albasa
  7. Kokomba
  8. Tumatir
  9. Gishiri
  10. Maggi

  Yadda ake hadawa

  1. To uwar’gida, da farko ki gyara wakenki ki wanke ki zuba a tukunya ki dora a wuta.
  2. Idan kin duba waken ya nuna sai ki wanke shinkafarki tas, sannan ki zuba a kan waken sai ki sa gishiri ki rufe.
  3. Sai ki dauko salat dinki ki wanke da gishiri, sannan ki yanka, ki wanke kokomba da tumatir da albasa suma ki yanka ki ajiye a gefe.
  4. Sai ki duba Idan shinkafarki tadahu sai ki sauke.
  5. Ki soya man gyada da albasa.
  6. Sai ki zuba a kula ko a filet ki sa manki, da su salat, da maggi, da yajinki sannan a ci.

  Na gode sosai sai mun sake haduwa a shiri  na gaba. Mai karatu na iya duba: Lemun mangwaro da dambun masara da makamantansu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): breaktime.ng

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All