Makalu

Lemun citta da lemun tsami a cikin sauki

 • Barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka. Yau za muyi hadin juice din lemun tsami da citta. Ga yadda ake yi kamar haka:
  Abubuwan hadawa

  1. Lemun tsami 6
  2. Citta 3
  3. Suga
  4. Abin kanshi (filabo)

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki wanke lemunki sai ki yanka ki matse ruwan a roba mai kyau.
  2. Sai ki wanke citta ki goga da abin goga kubewa sai ki sa ruwa.
  3. Sai ki tace da rariya mai laushi ki hada da lemon tsaminki
  4. Sannan ki zuba sugar da abin kamshi ki juyashi sosai .
  5. Sai ki sa a jug ki sa kankara ko kisa a firinji.

  A sha dadi lafiya. Na barku lafiya, sai haduwa na gaba in Allah Ya yarda. Sannan za a iya duba: Dahuwar shinkafa da wake da kuma lemun mangwaro da makamantansu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Hanyoyi guda biyar na rage ƙiba ba tare da an shiga hatsari ba

  Posted Jun 12

  A duniyarmu ta yau, ƙiba na daya daga cikin matsalolin da ke addabar mutane da dama. Saboda irin ci gaba da aka samu na yawaitar abinci kala-kala – abincin gargajiya da na zamani, na gwangwani da na gona – ya sa da yawa mutane na yawaita cin abincin da zai k...

 • Sharudda da kuma ladubbar sallar idi karama

  Posted Jun 3

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da iyalansa da Sahabbansa baki daya. Idi shine duk abinda yake dawowa yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci, kamar sati-sati, ko wata-wata, ko shekara-shekara. Shar'anta s...

 • Hukunce-hukuncen zakkar fidda kai

  Posted May 31

  Ma'anar zakkar fidda kai: Sadaka ce wacce ake bayar da ita sakamakon kammala azumin watan Ramadan. An shar'anta zakkar ne a shekara ta biyu bayan hijirar Annabi sallallahu alaihi wa sallam daga Makkah zuwa Madinah, a shekarar da aka wajabta azumin watan Ramadan. Huku...

 • Yadda ake hada local jollof rice

  Posted May 30

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Barka da shan ruwa. Yau zamu koyi yadda ake hada local jollof rice wato dafa dukan shinkafa ke nan da Hausa. Abubuwan hadawa Shinkafa Tattasai da tarugu Daddawa Albasa Seasoning Manja Ta...

 • Yadda ake hada bitter leaf soup

  Posted May 30

  Assalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya na yau. Barka da shan ruwa. A yau zamu duba yadda za ki hada bitter leaf soup (miyan shuwaka). Abubuwan hadawa Manja Nama Seasoning Garlic  Ginger Shuwaka (bitter leaf) Tattasai Ta...

View All