Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake dubulan

 • Abubuwan hadawa

  1. Fulawa
  2. Baking powder
  3. Kwai
  4. Suga
  5. Lemon tsami

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki tankade fulawarki a roba mai dan fadi sai ki zuba bakin hoda da kwai sai ki kwaba fulawarki kamar na cincin kwabin ya yi laushi yanda za ki iya murza shi.
  2. Sai ki shafa mai kadan a tire, sannan ki murza shi ya yi tsayi, sai ki nade shi kamar triangle, ki cusa bakin a cikin dayan, haka za ki tayi har ki gama.
  3. Idan kin gama sai ki dora kaskonki a wuta, ki sa manki idan ya yi zafi, sai ki zuba ki soya, idan kin gama soyawa sai ki sauke man.
  4. Sai ki zuba suga a tukunya mai kyau, sanna ki zuba suga da ruwa kadan sai ki sa lemon tsami ki dafa sugan idan ya tafasa sai ki sauke, ki zuba akan Dubulan dinki, ki zuba ko Ina ya ji sosai.

  Na gode. Sannan mai karatu za iya duba: Yadda ake miyar kori da yadda ake fritters da sauransu.

Comments

0 comments