Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake hada miyar karkashi

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka.
  Yau za muyi miyar karkashi.

  Abubuwan hadawa

  1. Karkashi danye
  2. Wake
  3. Nama ko kifi
  4. Attarugu
  5. Albasa
  6. Magi
  7. Toka
  8. Citta da tafarnuwa
  9. Nikakken gyada
  10. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki wanke namanki ki yanka albasa ki sa maggi tafarnuwa da gishiri ki dora a wuta ki tafasa shi.
  2. Sai ki dauko karkashinki ki yanka, sai ki duba idan namanki ya tafasa sai ki sauke, ki gyara wakenki, ki zuba a tukunya, ki dora a wuta.
  3. Sai ki jajjaga attarugunki da albasa, sai ki kwashe ki daka citta da tafarnuwa da daddawa sai ki zuba akan waken idan ya dahu sai ki zuba karkashinki ki sa nama da toka kadan.
  4. Idan kin bashi minti goma sai ki duba ki zuba gyadarki ki juya, sai ki rufe idan ya yi sai ki sauke ki sa magi da gishiri. Shikenan Miya ta hadu.

  Abin lura

  Ba’a sawa karkashi mai sannan ana sa maggi ne bayan an sauke domin ba a son ya tsike.

  Na gode, taku a kullum Rabi’at Muhammad Babanyaya. Sannan mai karatu na iya duba: Miyar shuwaka da yadda ake spring rolls 

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): Aminiya (Daily Trust)

Comments

1 comment