Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake miyar shuwaka

 • Abubuwan hadawa

  1. Shuwaka
  2. Nama da kifi
  3. Tattasai 4
  4. Attarugu 6
  5. Albasa 2
  6. Magi 10
  7. Man ja
  8. Gyada ko agushi
  9. Gishiri
  10. Tafarnuwa

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko zaki wanke shuwakarki da kanwa ko ki tafasa ki wanke ki cire dacin yanda za ki iya ci.
  2. Sai ki wanke namanki ki yanka albasa ki sa maggi da tafarnuwa da gishiri ki dora a wuta ki tafasa shi idan ya yi sai ki sauke ki soya sama sama.
  3. Sai ki jajjaga kayan miyarki, sannan ki soya idan ya yi, sai ki zuba ruwa ki sa maggi da tafarnuwa da citta, ki zuba namanki sai ki wanke kifi ki zuba ki rufe ya samu minti sha bayar.
  4. Idan ya yi sai ki zuba shuwakarki da kika wanke, sannan ki juyashi sosai sai ki dan dana ki ji dandano ya yi sai ki rufe ya yi minti bayar.
  5. Sai ki zuba agushi ko gyada sai ki juya sosai ki rufe ya yi minti biyu sai ki sauke. Ki ci da irin tuwon da kike bukata.

  Na gode. Sannan mai karatu na iya duba: Miyar karkashi da egg rolls da makamantansu.

  Hakkin mallakan hoto (photo credit): st-evemagazine

Comments

1 comment