Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake hada egg Rolls

 • Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da sake haduwa a cikin wannan fili mai albarka da fatan iyali suna lafiya, ya sanyi Allah ya nuna mana wucewarsa lafiya

  Abubuwan hadawa

  1. Filawa  kofi 3
  2. Simas 1
  3. Kwai 5
  4. Suga
  5. Bakin hoda
  6. Man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko uwargida za ki tankade fulawarki a roba mai dan fadi sai ki zuba bakin hoda da simas sai ki juyashi sosai ya hadu.
  2. Sannan ki jika sugarki da ruwa idan ya jika sai ki kwaba fulawarki kamar na cincin wabin yayi laushi yanda za ki iya murzashi a tire.
  3. Sai ki dafa kwanki ki bare idan kin mirza fulawar ya yi fadi sai ki dauko kwai daya ki sa, daga nan sai ki nade ki mulmula kamar ball, haka zaki tayi harki gama.
  4. Idan kin gama sai ki dora kaskonki a wuta ki sa manki Idan ya yi zafi sai ki zuba ki soya kar ki sa wuta da yawa Idan kingama sai ki kwashe ki zubawa maigida da yara.

  Na gode, bissalam. Sannan mai karatu na iya duba: Yadda ake spring rolls da tamarind juice lemun tsamiya da makamantansu.

Comments

0 comments