Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake hada guava juice

 • Abubuwan hadawa

  1. Gwaiba
  2. Lemun tsami
  3. Suga
  4. Flavour

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki wanke gwaibarki ki yanka kanana ki zuba a blender ki markada, sannan sai ki tace.
  2. Idan kin tace sai ki dauko lemun tsaminki, sai ki wanke ki yanka sai ki matse ki tace akan gwaibarki.
  3. Sai ki zuba suga da flavour ki juya shi sosai sannan ki dan dana ki ji suga ko yayi. Idan kin gama sai ki saka kankara ko ki sa a firinji ya yi sanyi. A sha dadi lafiya

  Na gode, sai anjima, taku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya. Sannan za a iya duba: Fruit-salad da egg rolls da sauransu.

Comments

0 comments