Makalu

Sabbin Makalu

View All

Yadda ake spring rolls

 • Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Nikakken nama
  3. Kabeji
  4. Karas
  5. Albasa
  6. Kwai
  7. Magi
  8. Gishiri
  9. Curry
  10. Brush
  11. Man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko, Uwargida zaki wanke kabejinki ki yanka da albasa da karas sanan ki soyasu da mai cokali daya, kuma suyan ya zamana sama-sama.
  2. Sannan sai ki zuba nikakken nama, da maggi, da gishiri da curry. Jim kadan sai ki sauke daga kan wuta.
  3. Bayan nan, sai ki hada filawa, kwai, maggi, gishiri da ruwa ki kwaba yayi kamar kaurin wainar filawa.
  4. Sai kuma ki shafa mai a nonstick, sannan ki shafa filawarki da brush. Idan ya yi, za ki ga gefen ya dago sai ki cire a gefe ki tara.
  5. Idan kin gama sai ki dinga dauka kina zuba hadin kabejinki kina nadewa kamar tabarma.
  6. Haka zaki yi tayi har ki gama. Idan kin gama sai ki sa kaskon suya a wuta ki sa manki, idan ya yi zafi sai ki soya.
  7. Idan kin gama soyawa sai ki kwashe ki sawa maigida ya je office dashi ko kuwa yara dan tafiya makaranta.

  Na gode. Ta ku a kullum Rabiat Muhammad Babanyaya. Sannan mai karatu na iya duba: Tamarind juice (lemun tsamiya) da fruit salad da sauransu.

Comments

1 comment