Makalu

Yadda ake soft peanut and coconut balls

 • Barkanmu da sake saduwa a fanninmu na girke-girke na Bakandamiya. A girkin namu na yau zamu koyar da yadda ake soft peanut and coconut balls. Amma kafinnan, mai karatu na iya duba girkinmu da muka koyar a baya, inda muka koyar da yadda ake cabbage sauce. To mai karatu, ga yadda ake soft peanut and coconut balls dalla dalla kamar haka:

  Abubuwan hadawa

  1. Gyada kofi1
  2. Kwakwa kofi ½
  3. Sugar kofi ¾
  4. Madara ta gari cokali 3 babba
  5. Man gyada ko butter cokali 1
  6. Ruwa cokali 1

  Yadda ake hadawa

  1. Ki gyara gyadan ki kidan cire bawon jikin, sai ki daka a turmi sama sama, ajiye a gefe.
  2. Dauko kwakwa ki cire bakin jikin, sai ki gurza shi a jikin abun goge kubewa, say ki ajiye a gefe.
  3. Ki daura non stick pan naki akan wuta (ki rage wutan) ki sa sugar sai ki na juyawa a hankali har sai sugar ya narke.
  4. Sai ki kawo ruwa ki sa ki juya, ki kawo man gyada ki sa ki juya sai ki dauko gyada ki zuba ki kawo kwakwa ki sa ki juya, sai ki kawo madara ki sa ki juya ki kashe wutanki.
  5. Ki shafa mai a jikin faranti sai ki juye hadin ki ki yi rolling na shi, sai ki na diban kadan kadan ki na mulmula da tafin hannu ki. A ci dadi lafiya.

  Wannan shine yadda ake soft peanut and coconut balls. Na gode, sai mun hadu a girki na gaba da yardan Allah. Amma kafin nan, mai karatu na iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake sponge pancakes da Yadda ake chocolate buns da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted Sat at 3:40 PM

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All