Makalu

Fish and boiled eggs sauce

 • A yau za mu koyi yadda ake fish and boiled egg sauce a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Mai karatu na iya duba girkinmu da muka koyar a baya mai suna, yadda ake ground beef sauce, za a iya dubawa kafin mu ci gaba. 

  Abubuwan hadawa

  1. Kifi (dafaffe)
  2. Kwai (dafaffe)
  3. Tumatir (ki yanka)
  4. Tarugu (ki jajjaga)
  5. Tattasai (ki yanka)
  6. Koren wake (ki yanka)
  7. Karas (ki yanka)
  8. Lawashi (ki yanka)
  9. Marasar gwangwani (ba dole bane)
  10. Kayan kamshi
  11. Maggi
  12. Mai
  13. Albasa
  14. Gishiri kadan

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko za ki dauko dafaffen kifinki ki cire iya zallar tsoka ki raba shi da kaya sai ki ajiye a gefe.
  2. Dauko dafaffen kwai shima ki yanka shi dan dai dai (karki yanka shi kanana sosai).
  3. Sai ki daura kasko ko tukunyarki akan wuta ki zuba mai ki yanka albasa ki soya sama sama sannan ki kawo tarugu da tattasai ki sa ki juya suma ki soya sama sama.
  4. Sannan ki kawo kayan kamshi, da maggi, da gishiri (iya dandanon da zai mi ki) ki sa ki juya, kawo tumatir ki sa ki juya a hankali sai ki rufe nadan wani lokaci kadan.
  5. Sai ki kawo kifi da kwanki ki zuba a ciki, ki juya sai ki rufe ki rage wuta sosai nadan wani lokaci kadan.
  6. Daga Karshe ki kawo su lawashi, da koren wake, da karas da masarar gwangwani ki zuba ki juya a hankali sai ki bari sudan turara kadan ki sauke. A na iya cin wannan sauce tare da shinkafa, ko taliya, ko soyayyen doya ko dankali da dai sauransu.

  Sannan za a iya duba girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake fried rice 2 da yadda ake tsiren kaza da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

  Posted Oct 19

  Asaalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu duba yadda uwargida za ta hada miyan masa, kuma wannan miyan za ki iya cin abubuwa dayawa ma da ita. Abubuwan hadawa Manja Albasa da lawashi Kayan miya Naman rago Allayaho...

 • Darasi game da electrical method

  Posted Oct 18

  A makala ta da ta gabata mai suna method of mixture na yi bayanin specific heat capacity yanda ya ke dauke da method guda biyu na measuring dinshi wanda na kawo su kamar haka: Method of mixtures Electrical Method Saboda haka method din lissafinsu ma biyu ne, kuma...

 • Yadda ake grilled sandwich

  Posted Oct 18

  Abubuwan hadawa Biredi mai yanka Soyayyen plantain(agada) Kwai Nama (ki dafa, ki daka) Tarugu (ki jajjaga ko ki yanka) Koren wake (ki yanka) Karas (ki yanka) Kabeji (ki yanka) Maggi Gishiri Butter Abun gashi (manual sandwich grill) Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada buttered shape cookies

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum, makalarmu ta yau zamu yi bayani ne akan yadda zaki hada butter shaped cookies Abubuwan hadawa Flour 2 cups Sugar 1 cup Butter 250grm Baking powder 1tspn Kwai 1 Icing sugar Egg white Yadda ake hadawa Farko za ki mixing sugar da butter n...

 • Yadda ake hada red velvet coconut balls

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Zamu yi bayani akan yadda za ki hada red velvet coconut balls a yau. Abubuwan hadawa Kwakwa Condensed milk Madarar gari Corn flour Red colour Yadda ake hadawa Farko za ki zuba corn ...

View All