Makalu

Yadda ake jollof na shinkafa da wake

 • A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake jollof na shinkafa da wake. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa
  2. Wake
  3. Kwai (dafaffe ki bare ki yanka kanana)
  4. Tarugu (ki jajjaga)
  5. Albasa (ki yanka)
  6. Tumatur mai kyau mai tauri (ki yanka kanana)
  7. Koren wake
  8. Peas
  9. Kayan kamshi
  10. Maggi

  Yadda ake hadawa

  1. Ki daura tukunya kan wuta ki sa ruwa, ki gyara waken ki, idan ruwanki ya dauko tafasa ki zuba waken ki a ciki ki sa gishiri kadan, sai ki rufe.
  2. Idan ya fara tafasa ya dan yi laushi kadan, wanke shinkafar ki zuba a cikin waken ki rufe nadan wani lokacin har sai sunyi rabin nuna. Sai ki sauke ki kara ruwa ki tace ki tsane shi ki ajiye a gefe.
  3. Wanke tukunyar ki kara maida ta wuta ki sa mai ki yanka albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugunki ki sa a ciki ki juya.
  4. Ki kawo kayan kamshi, da maggi (iya dandanon da zai miki ki sa), sai ki kara ruwa (iya wanda zai karasa mi ki shinkafar ki. Sai ki rufe nadan wani lokacin har sai ya tafaso.
  5. Sai ki kawo shinkafa da waken ki zuba a ciki sannan ki juya a hankali ki ki rufe nadan wani lokacin har sai ruwan ya shanye sai ki kawo su peas, koren wake ki sa ki juya ki rufe sudan turara sai ki sauke ki kawo kwanki da tumatir ki sa ki juya a hankali sai ki zuba a plate.

  Za a iya duba: Yadda ake meat pie da yadda ake couscous jollof da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake hada shredded chicken sauce

  Posted Feb 11

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Inda yau zan gabatar da yadda ake hada shredded chicken sauce. A baya munyi bayani akan yadda za ki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fried rice da sauran su. Za a iya dubawa....

 • Yadda ake hada potatoe soup

  Posted Feb 11

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan gabatar da yadda ake hada potatoe soup. A baya munyi bayani akan yadda zaki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fries rice da sauran su. Abubuwan hadawa Dankali (i...

 • Yadda ake hada turmeric fried rice

  Posted Feb 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zanu koyar da yadda ake hada turmeric fried rice. Abubuwan hadawa Turmeric Curry Albasa da lawashi Rice Man gyada  Tarugu Green pepper Carrots Green beans Peas Garlic ...

 • Yadda ake hada cabbage sauce

  Posted Feb 11

  Barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau kuma zamu koyar da yadda ake hada cabbage sauce. A baya munyi bayanin akan yadda ake abinci daban-daban, za a iya dubawa. Abubuwan hadawa Cabbage Green pepper Peas Green beans Tarugu Tattasai S...

 • Yadda ake hada vegetable rice

  Posted Feb 11

  Barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Yau zan gabatar mana da yadda ake hada vegetable rice. Abubuwan hadawa Peas Green beans Carrots Inibi Basmati rice/Ko normal shinkafa dangote Yadda ake hadawa Farko idan basmati rice za ki yi amf...

View All