Makalu

Yadda ake pasta jollof

 • A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake pasta jollof. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Taliya
  2. Macaroni
  3. Tarugu
  4. Albasa
  5. Peas
  6. Karas
  7. Lawashi
  8. Mai
  9. Maggi
  10. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Daura tukunya babba akan wuta ki sa ruwa idan ya tafasa dauko taliya da macaroni ki sa gishiri kadan a ciki ki barshi nadan wani lokacin har sai ya yi rabin dahuwa sai ki kara ruwa ki tsane sa a matsani. Ajiye a gefe.
  2. Sake daura tukunya ki sa mai ki kawo albasa ki yanka ki soya sama sama sai ki kawo tarugu ki sa ki soya sama sama, ki sa maggi, da kayan kamshi, ki tsaida ruwa dai dai wanda zai karasa miki dahuwanki. Ki rufe ki barshi nadan wani lokacin.
  3. Sai ki kawo su taliyar ki zuba a ciki ki juya ki rufe nadan wani lokacin har sai ruwan ciki ya shanye dauko karas, da peas ki sa ki barsu su turara sai ki sauke. A ci dadi lafiya.

  Za a iya duba: Yadda ake couscous jollof da yadda ake dankali da kwai da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Yadda ake hada spinach soup (miyan masa)

  Posted Oct 19

  Asaalamu alaikum, barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu duba yadda uwargida za ta hada miyan masa, kuma wannan miyan za ki iya cin abubuwa dayawa ma da ita. Abubuwan hadawa Manja Albasa da lawashi Kayan miya Naman rago Allayaho...

 • Darasi game da electrical method

  Posted Oct 18

  A makala ta da ta gabata mai suna method of mixture na yi bayanin specific heat capacity yanda ya ke dauke da method guda biyu na measuring dinshi wanda na kawo su kamar haka: Method of mixtures Electrical Method Saboda haka method din lissafinsu ma biyu ne, kuma...

 • Yadda ake grilled sandwich

  Posted Oct 18

  Abubuwan hadawa Biredi mai yanka Soyayyen plantain(agada) Kwai Nama (ki dafa, ki daka) Tarugu (ki jajjaga ko ki yanka) Koren wake (ki yanka) Karas (ki yanka) Kabeji (ki yanka) Maggi Gishiri Butter Abun gashi (manual sandwich grill) Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada buttered shape cookies

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum, makalarmu ta yau zamu yi bayani ne akan yadda zaki hada butter shaped cookies Abubuwan hadawa Flour 2 cups Sugar 1 cup Butter 250grm Baking powder 1tspn Kwai 1 Icing sugar Egg white Yadda ake hadawa Farko za ki mixing sugar da butter n...

 • Yadda ake hada red velvet coconut balls

  Posted Oct 14

  Assalamu alaikum barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. Zamu yi bayani akan yadda za ki hada red velvet coconut balls a yau. Abubuwan hadawa Kwakwa Condensed milk Madarar gari Corn flour Red colour Yadda ake hadawa Farko za ki zuba corn ...

View All