Makalu

Yanda ake gozleme

 • A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake gozleme. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Filawa
  2. Yeast
  3. Gishiri kadan
  4. Butter
  5. Ruwa kadan
  6. Tsokan nama ko na tsokan kirjin kaza
  7. Koren tattasai (ki yanka)
  8. Kabeji
  9. Tarugu (ki jajjaga)
  10. Kayan kamshi
  11. Maggi
  12. Karas (ki gyara ki gurza)
  13. Lawashi (ki yanka)

  Yadda ake hadawa

  1. Dauko roba mai dan girma ki kawo filawa ki tankade, gishiri kadan ki sa ki kawo yeast na ki ki sa sai ki kawo ruwa ko ruwan dimi ki sa dan dai dai kisa (kar ki sa ruwa sosai kamar kwabin paratha za ki yi shi ). Ki kwaba ya kwabu sosai sannan ki rufe ki sa a rana ya taso nadan wani lokaci.
  2. Kafin ya taso sai ki hada abin sawa a ciki. Daura kasko akan wuta ki sa mai kadan ki kawo albasa da tarugu ki sa ki soya sama sama sai ki kawo tsokar kazar ki ki sa ki sa ruwa kadan ki juya ki kawo kayan kamshi da maggi, da gishiri kadan ki sa ki juya sannan ki rufe nadan wani lokaci har sai ruwan ya shanye (ruwan kadan za ki yayyafa akai fa badayawa ba) sannan ki kawo karas na ki da koren tattasai, da kabeji shima ki sa ki rufe ki barsu, su turara sai ki sauke. Ajiye a gefe.
  3. Dauko kwabin filawanki ki na diban kadan kadan kina fadada shi sosai har sai ya yi fale-fale sai ki kawo marfin kwano ko wani abu mai round baki sai ki kifa akan filawa ki fidda shape na sa ya baki round sannan ki kawo hadin kazar ki ki sa a tsakiya sai ki shafa ruwa a baki bakin sai ki dauko dayan gefen ki rufa akai ki danna da karshen (edges) da hannun ki a hankali haka za ki yi har sai kin gama da sauran filawa da hadin kazar ki. Ajiye a gefe.
  4. Daura nan stick pan akan wuta (wutan ba sosai ba) kina gasawa kina juyawa har sai ya gasu baki daya sai ki sauke ki shafa masa butter ajiki. Ajiye a gefe har sai kin gama da sauran. A ci dadi lafiya.

  Sannan za a iya dubaYadda ake local jollof rice da yadda ake chinese spaghetti da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

 • Nazari bisa zamantakewar Hausawa na jiya da yau

  Posted May 14

  Tsakure Hausawa kan ce wanda ya tuna bara bai ji dadin bana ba. Haƙiƙa zamantakewar Hausawa a da ta kasance gwanin ban sha’awa. A da, Hausawa sun kasance suna zama ne na cuɗe-ni-in-cuɗe-ka. Wannan ne ma ya sanya tsarin muhallin Bahaushe a da bai kasance ramin-kur...

 • Hanyoyi uku da za a magance illar ƙiba ga yara 'yan shekaru 13-18

  Posted May 11

  Kamar yadda ƙungiyar kula da lafiya ta duniya (2012) ta nuna cewa, shekaru talatin (30) da suka gabata an samu ƙaruwar mutane miliyan ɗari da saba'in (170 million) da suka abka cikin matsalar ƙiba wanda kuwa mafiya yawa yara ne 'yan shekaru ƙasa da sha takwas ne (18). W...

View All