Makalu

Yadda ake dambun couscous cikin sauki

 • A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake dambun couscous cikin sauki. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Couscous
  2. Zogale (ki gyara ki wanke)
  3. Dafaffen nama (ki yanka kanana)
  4. Man gyada
  5. Garin karago
  6. Tarugu(ki jajjaga)
  7. Albasa (ki yanka)
  8. Attasai (ki yanka kanana (karas (ki yanka)
  9. Koren wake (ki yanka kanana)
  10. Kayan kamshi
  11. Maggi
  12. Gishiri

  Yadda ake hadawa

  1. Dauko couscous na ki ki zuba mi shi man gyada ki juya. Ajiye a gefe.
  2. Dauko turmi zuba garin karagonki, yanka tarugu da albasa ki sa maggi dan daidai ki dake su sai ki kwashe. Ajiye a gefe.
  3. Dauko albasa da tattasai ki yanka kanana. Ajiye a gefe.
  4. Daura tukunya akan wuta ki sa ruwa dan daidai (yanda zai dafa/turara miki couscous na ki) sannan ki kawo tarugu, da albasa, da kayan kamshi, da maggi (iya dandanon da zai miki), da gishiri kadan, ki juya, ki kawo nama da zogalen ki zuba ki rufe tukunyar ki, ki barta har sai ya tafaso sannan ki kawo couscous na ki ki zuba ki juya a hankali.
  5. Kawo karas da koren wake ki sa ki juya a hankali sai ki rufe su turara (ki tabbatar kin rage wuta) idan ya turaru sai ki sauke ki kawo yankakkiyar albasa ki da tattasai ki sa ji juya ki kawo hadin garin karagon ki ki barbada a hankali ki na juya har sai garin karagon ya kare sai ki zuba a plate. A ci dadi lafiya.

  Za a iya dubaYadda ake chinese spaghetti da yadda ake local jollof rice da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted Sat at 3:40 PM

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All