Makalu

Yadda ake beef samosa, meat pie, spring roll filling

 • A fannin girke girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake beef samosa, meat pie, spring roll  filling. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Dafaffen nama (daka a turmi)
  2. Tarugu (ki jajjaga)
  3. Karas (ki yanka kanana)
  4. Koren wake (ki yanka kanana)
  5. Albasa (ki yanka)
  6. Kayan kamshi
  7. Maggi

  Yadda ake hadawa

  1. Da farko ki daura kasko ko tukunya akan wuta, ki zuba mai kadan, kawo tarugu, ki sa albasa, ki hada sai ki juya.
  2. Kawo nama (wanda aka riga aka daka a turmi) ki sa a ciki sai ki yayyafa ruwa kadan a kai.
  3. Ki kawo maggi da kayan kamshi ki sa ki juya. Ki rufe ki bar shi nadan wani lokaci. Ki rage wuta.
  4. Daga karshe, ki kawo koren wake da karas ki sa ki juya ki rufe, su dan turara a ciki sai ki sauke. Wannan filling za ki iya yin samosa, ko meat pie da dai sauransu da shi.

  Dubi: Yadda ake plantain sauce da yadda ake dambun couscous cikin sauki da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

  Posted Sep 2

  A ‘yan shekaru kadan da suka wuce, kafar yada labarai ta kasar Amurka mai suna USA Today ta ruwaito cewa kashi 50% na mutanen kasar Amurka suna ta kokarin su ga sun inganta lafiyarsu ta hanyar kokarin ganin sun rage yadda su ke cin nama da yawa a ciki abincinsu. A...

 • Physics: Darasi akan pressure in fluid

  Posted Aug 29

  Ga definition na pressure a Turance kamar haka; pressure is defined as the force acting perpendicularly per unit area. Idan kuma za a duba equation na shi ne a math, shi kuma ga shi kamar haka: Pressure = Force / Area , shi ne kamar haka,  P = F / A Ga abinda ...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Aug 25

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ...

 • Wa ya gaya mi ki cewa yana son ki har cikin zuciyarsa? Ki lura da wadannan alamomi

  Posted Aug 24

  Abu ne mai matuƙar ciwo mace ta fahimci cewa namijin da take so, baya sonta. Baya son kasancewa da ita a rayuwarsa.  Abun takaici irin wadannan mazajen basa iya fadar cewa ba sa son mace a baki, bare har ta san inda dare ya yi ma ta. Sai ya zamo ke a zuciyar ki ki...

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Aug 20

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

View All