Makalu

Yadda ake cabbage jollof rice

 • A fannin girke girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake cabbage jollof rice. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya.

  Abubuwan hadawa

  1. Tafashashshen shinkafa
  2. Kifi (ki dafa, ki bare, ki cire qaya)
  3. Kabeje (ki yanka, ki wanke, ki tsane)
  4. Albasa (ki yanka)
  5. Dafaffen kwai (ki yanka kanana)
  6. Tarugu (ki jajjaga)
  7. Kayan kamshi
  8. Daddawa (mai kyau)
  9. Maggi
  10. Mai
  11. Gishiri kadan

  Yadda ake hadawa

  1. Dauko kabeji ki yanka, ki yanka albasa a kai sannan ki sa vinegar ki wanke sai ki tsane a matsani. Ajiye a gefe.
  2. Daura tukunya, ki sa mai ki kawo albasa tarugu da daddawa, da kayan kamshi, da gishiri da maggi iya dandanon da zai mi ki ki sa, ki juya ki soya sama sama.
  3. Sai ki tsaida ruwa kamar kofi biyu. Ki bar shi ya yi ta tafasa har sai ya hade jikinsa. Ki bari har sai ruwan ya yi daidai yadda zai karasa miki dafa shinkafanki.
  4. Ki bar shi ya tafaso sannan ki kawo shinkafarki ki sa, ki kawo kifi da kwanki ki sa sai ki juya, ki rufe ta har sai ruwan ya shanye sai ki kawo kabejin ki wanda ki ka yanka ki sa ki juya a hankali sai ki rufe, su turaru sai ki sauke ki sa a plate.
  5. Za ki iya kara yanka latas ko kabejin ko ki yanka tomatur a kai. A ci dadi lafiya.

  DubiYanda ake beef samosa meat pie spring roll filling da yadda ake plantain sauce da sauransu.

Comments

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Dalilan da ka iya sawa a koma vegan diet

  Posted Sep 2

  A ‘yan shekaru kadan da suka wuce, kafar yada labarai ta kasar Amurka mai suna USA Today ta ruwaito cewa kashi 50% na mutanen kasar Amurka suna ta kokarin su ga sun inganta lafiyarsu ta hanyar kokarin ganin sun rage yadda su ke cin nama da yawa a ciki abincinsu. A...

 • Physics: Darasi akan pressure in fluid

  Posted Aug 29

  Ga definition na pressure a Turance kamar haka; pressure is defined as the force acting perpendicularly per unit area. Idan kuma za a duba equation na shi ne a math, shi kuma ga shi kamar haka: Pressure = Force / Area , shi ne kamar haka,  P = F / A Ga abinda ...

 • Matsalar shaye-shaye a tsakanin matasanmu a yau

  Posted Aug 25

  A wannan Makala za muyi dubi ne zuwa ga wani maudu’i mai muhimmanincin gaske. Za mu duba matsalar shaye-shaye da ya zama tamkar ruwan dare gama duniya a tsakanin matasanmu maza har da mata a wannan zamani. Duk da cewa wannan mummunar dabi’a ba dabi’a ...

 • Wa ya gaya mi ki cewa yana son ki har cikin zuciyarsa? Ki lura da wadannan alamomi

  Posted Aug 24

  Abu ne mai matuƙar ciwo mace ta fahimci cewa namijin da take so, baya sonta. Baya son kasancewa da ita a rayuwarsa.  Abun takaici irin wadannan mazajen basa iya fadar cewa ba sa son mace a baki, bare har ta san inda dare ya yi ma ta. Sai ya zamo ke a zuciyar ki ki...

 • Maɗigo da yawaitarsa cikin al’umma: Ina mafita?

  Posted Aug 20

  Tasowarmu muna kanana cikin alumma mun ga iyayenmu da sauran magabata suna da aure. Kowa da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Hakanan kuma yayin da muke rayuwa mun ga ‘yan mata da samari daban-daban sun taso kuma mun ga sun yi aure. Kuma sannan sa’i da lokaci mutu...

View All