Makalu

Yadda ake miyar taushe

 • Abubuwan Hadawa

  1. Dafaffen nama da soyayyen nama
  2. Alayyaho da yakuwa (ki wanke da gishiri ki sa a colender ya tsane)
  3. Markadadden gyada (irin na kunun gyada)
  4. Albasa
  5. Grated tarugu da albasa
  6. Maggi da gishiri
  7. Kayan yaji (spices)
  8. Manja da man gyada

  Yadda ake hadawa

  1. Ki sami wukanki ki yanka dafaffafen namanki kisa a gefe
  2. Sai ki dauko gyada ki kisa mata ruwa ki dama ta, itama ki ajiye a gefe
  3. Sannan kisa tukunyarki akan wuta kisa manja da man gyadarki
  4. Sai ki dauko albasa kisa, amma ki soya shi sama-sama
  5. Yanzu sai ki dauko namanki da kika yanka kisa aciki ki soya sama-sama
  6. Sai ki dauko grated tarugunki kisa aciki sannan ki juya
  7. Ki kawo Maggi da curry da kayan yaji (spices) ki sa
  8. Bayan haka, sai ki kawo soyayyen namanki ki sa sai ki juya
  9. Sai ki tsaida ruwa kadan ki rufe tukunyarki na dan wani har sai kin ji ya fara tafasa
  10. Sannan sai ki dauko ganyen ki kisa aciki ki juya ki rufe shi na dan wani lokaci
  11. Ki dauko gyadarki (wanda kika dama) kisa aciki, sannan ki juya miyarki ki sake rufewa ki barta na dan wani lokaci
  12. Daga karshe, sai ki sauke miyan ki

  Zaki iya ci da couscous (kamar yanda kika gani a hoto) ko kuma da tuwon shinkafa ko semo da makamantansu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted Sat at 3:40 PM

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted Thu at 12:18 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All