Makalu

Yadda ake suya ko tsire

 • Abubuwan Hadawa

  1. Nama(marar kitse)
  2. Yaji (ki sa Kayan qamshi Kamar su citta, kaninfari Maggi, daddawa, da saukan kayan kamshi da kike bukata)
  3. Man miya (veg oil)
  4. Albasa
  5. Garin citta
  6. Maggi (na ruwa)
  7. Gishiri
  8. Clingfilm
  9. Foil paper
  10. Skewers (toothpicks)
  11. Koren tattasai
  12. Yellow tattasai
  13. Kwakwamba (Cucumber)
  14. Albasa (na garnishing)

  Yadda ake hadawa

  1. Ki sami namanki, ki wanke ki gyara shi, sai ki yanka shi dogo dogo.
  2. Sai ki yanka albasa
  3. Ki kawo su yajin ki da maggi
  4. Ki dauko garin citta da sauran kayan kamshinki (spices) ki sa a kai
  5. Sai ki gauraya komai ya shiga jikin sa
  6. Ki dauko clingfilm Ki Rufe Namanki
  7. Sai ki sa a fridge ki barshi yayi Kamar awa hudu ko ki barshi ya kwana a fridge.
  8. Ki dauko marinated namanki ki sa a foil paper saiki sa a preheated oven ki gasa shi kamar na minti 30.
  9. Sannan sai ki fitar Daga oven ki baxa shi ya sha iska, sai ki yan yanka shi.
  10. Sai ki dauko yajinki da Maggi mai ruwanki  ki kara sawa akai ki dauko tsinken nama ki gera su a jiki sai ki yaryada kadan a jikin nama sannan ki Mayar oven ki gasa (kina juyawa don kar ya kone ta gefe daya ). Ga wacce ba ta da oven kuma, za ki iyi daura non.Stick pan naki akan wuta ki gasa.

  Sannan za ki iya duba wasu daga cikin girke girkenmu na baya, kamar: Yadda ake miyar kwai da yadda ake kwadon latas da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted Wed at 1:07 PM

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted Mon at 1:07 PM

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

 • Jaye karar tsana: Uzuri da tuni daga mantuwa

  Posted May 16

  Ta Abu-Ubaida SANI Department of Languages and Cultures Federal University Gusau, Zamfara Phone No: 08133529736 Email: abuubaidasani5@gmail.com   1. Ya Allah mahalaccin komai,                  Wanda ya ƙaga yawan...

 • Kadan daga cikin falalar azumin watan Ramalana

  Posted May 14

  Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu da kyautata. Yana daga hikimar Allah Madaukakin Sarki fifita wasu mutane akan wasu, Ya kuma fifita wasu wurare aka...

View All