Makalu

Yadda ake hada natural zobo drink

 • Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakndamiya. A yau nazo maku da yadda ake hada fruity zobo, za ki iya yin shi saboda sana'a ko kuma domin sha a gida. Ga yadda za ki hada:

  Abubuwan hadawa

  1. Zobo
  2. Sugar
  3. Abarba
  4. Lemu
  5. Foster clerks
  6. Berries (tiara)
  7. Flavour (Vanilla ko strawberry)

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba sobo a cikin tukunya ki sa mi shi ruwa. Sai ki fere abarba ki sa bawonta a cikin dahuwar sobon ki nika abarba ki tace ruwanta ki ajiye a gefe.
  2. Sauran tukar ki sake maida su a cikin ruwan dahuwar sobo. Za ki dafa sobon nan na ki har ya tafasa. Sai ki tace shi ki sa awani wuri.
  3. Ki kawo ruwan abarba da ki ka nika ki zuba su a ciki ki sa sugar a ciki sai ki sake zubawa a pot ki mayar ya yi ta dahuwa kaman mintina 10.
  4. A sauke yadan sha iska sai ki sa flavour da foster clerk dinki a ciki. A sa kankara a sha, ko a sa shi a fridge.

  Sannan za a iya duba: yadda ake mango and banana smoothie da lemon cucumber drink da makantansu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake pasta jollof

  Posted Feb 16

  A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake pasta jollof. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya. Abubuwan hadawa Taliya Macaroni Tarugu Albasa Peas Karas Lawashi Mai Maggi ...

 • Yanda ake plantain vegetable rice

  Posted Feb 16

  A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake plantain vegetable rice. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya. Abubuwan hadawa Tafashashshen shinkafa Agada (plantain) Karas Koren w...

 • Yadda ake hada potatoe balls

  Posted Feb 11

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Inda yau zan gabatar da yadda ake hada potatoe balls, in ba'a manta ba a baya munyi bayani akan yadda za ki hada shredded chicken sauce da wadansu miyoyi na zamani. Abubuwan hadawa Potato...

 • Yadda ake hada shredded chicken sauce

  Posted Feb 11

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Inda yau zan gabatar da yadda ake hada shredded chicken sauce. A baya munyi bayani akan yadda za ki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fried rice da sauran su. Za a iya dubawa....

 • Yadda ake hada potatoe soup

  Posted Feb 11

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan gabatar da yadda ake hada potatoe soup. A baya munyi bayani akan yadda zaki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fries rice da sauran su. Abubuwan hadawa Dankali (i...

View All