Makalu

Yadda ake hada chicken pizza a gida

 • Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zamu koyar da yadda ake hada chicken pizza a gida, kada kuma uwargida ta manta, za ta iya duba darussanmu na baya kafin mu ci gaba.

  Abubuwan hadawa

  1. Filawa kofi 3 
  2. Gishiri cokali 1 (tspn)
  3. Yeast cokali 2 (tblspn)
  4. Ruwan dumi kofi daya 
  5. Gram masala cokali 1 (tspn)
  6. Sugar 

  Fillings

  1. Shredded chicken
  2. Ketch up
  3. Green Pepper
  4. Carrots and any desired veg mozzarella cheese(grated)

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki hada yeast dinki da sugar ki bar shi ya tashi.
  2. A cikin wani bowl ki sa flour, gishiri garam masala a ciki ki juya. Ki dauko yeast mixture ki zuba sai ki juya shi ko ki sa mixer ki hade idan ya hadu kinyi rolling sai ki sa a pizza tray ko pizza pan dinki.
  3. Ki shafa Ketchup ko tomatoe paste na ki akai sai ki barbada cheese ki sa vegies dinki akai da chicken ko beef sai ki sake saka cheese akai. A gasa a oven na tsawon mintina 15. Aci lafiya

  Sannan za a iya duba: Yadda ake hada natural zobo drink da kuma yadda ake hada sinasir da makamantansu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Magani da wasu alfanun ganyen Bi-ni-da-zuga (Jatropha Curcas)

  Posted Wed at 8:34 PM

  Alfanun tsiro ko ganye a matsayin abinci ko hanya ta samar da waraka (magani) daga wasu nau’o’in cututtuka ga ɗan Adam daɗɗaɗe abu ne a tarihi. Don haka, kusan kowace al’umma ta tanadar da hanyoyin sarrafa nau’ukan abincinta da kuma samar da kari...

 • Bayanai game da Boyle's Law

  Posted Mon at 7:09 PM

  Boyle’s law yana daya daga cikin laws na gas wanda a makala ta da ta gabata na yi bayani akai. Kamar yadda na fada a baya, a yau kuma zamu je kai tsaye ne don duba daya daga cikin gas laws. Wannan law din shine boyle’s law. Wani lokaci akan kira bo...

 • Abubuwan da dalibanmu ya kamata su sani kafin rubuta JAMB, WAEC da NECO

  Posted Apr 12

  A yau za mu ci gaba ne da tattaunawarmu akan jarabawar JAMB da muka faro a baya. Idan mai karatu na bukatar sanin abinda muka yi a baya zai iya duba inda muka tattauna akan Ire-iren matsalolin da dalibai ke fuskanta game da jarabawar JAMB. Insha Allah za mu ci gab...

 • Hanyoyi biyar (5) da za a bi don rage damuwa (anxiety)

  Posted Apr 10

  Zamu iya cewa duk wani dan adam da Allah ya hallita a doron kasa yana da wani abinda ya ke tsoro. Wannan tsoro kuwa shine akasarin lokaci ke jawo abinnan da ake kira a Turance da anxiety attack (damuwa mai tsanani) ko kuma panic attack. Anxiety ko damuwa mai tsanani wan...

 • Yadda ake hada apple smoothie

  Posted Apr 8

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Harwa yau mai karatu zai iya duba makalunmu da muka gabatar na daruruwan girke-girke a baya. A yau kuma zan koya mana yadda ake hada apple smoothie. Abubuwan hadawa Apple (tufa) Sugar ...

View All