Makalu

Yadda ake hada Indian fried rice

 • Assalamu Alaikum, barkanmu da sake saduwa a fannin girke-girke na Bakandamiya. A yau kuma zan nuna mana yadda ake hada indian fried rice ne. Wannan fried rice din hadi ne na vegetables na kasar India da Chinese. Dahuwar shinkafa ce a saukake, wadda za a iya ci da rana ko ma dare. Wannan recipe nawa ne da ya zama abinci mafi soyuwa a iyali na.

  Abubuwan hadawa

  1. Shinkafa (in son samu ne a sa basmati rice)
  2. Tarugu (chopped)
  3. Yankakkun ja da koren tattasai
  4. Lawashi (za ki bukaci mai dan yawa)
  5. Maggi
  6. Seasoning
  7. Gishiri
  8. Carrot
  9. Green peas
  10. Green beans
  11. Fennel Seeds
  12. Coriander
  13. Qwau Lemun tsami
  14. Mai ko bota

  Ina fata uwar gida ta hadda komai ,

  Yadda ake hadawa

  1. Ki sa mai a cikin tukunya, sai ki sa yankeken albasa ki idan ya yi zafi ki sa tarugu da slices na ja da green din tattasai ki juya kaman mintina sai ki sa lawashin albasa ki sake juyawa na kusan mintina.
  2. Sai ki sa karas, da peas, da green bean. Ki rufe ki bar shi kaman tsawon mintina biyar dan ya sulala a hankali ki sa duka seasoning, da spices da chillies na ki a hankali ki na zuba per boil rice ko basmati a ciki har sai ya hade.
  3. Idan kina yin na mutane da yawa ne dole za ki raba shi a wannan stage sai ki juya ki hade. Ki yayyafa ruwa ki barta ta gama dahuwa akan wuta ba sosai ba za ki fasa kwai ki zuba a ciki ki na juyawa har sai kwan ya hade.
  4. Ki matse lemun tsamin ki a ciki ki sake juyawa. Ki ci da irin salad din da ki ke so. A ci lafiya.

  Sannan za a iya dubaYadda ake hada chicken pizza a gida da yadda ake hada savoury stuffed yam balls da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake pasta jollof

  Posted Feb 16

  A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake pasta jollof. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya. Abubuwan hadawa Taliya Macaroni Tarugu Albasa Peas Karas Lawashi Mai Maggi ...

 • Yanda ake plantain vegetable rice

  Posted Feb 16

  A fannin girken girkenmu na Bakandamiya, yau za mu koyi yadda ake plantain vegetable rice. Sannan kar a manta, idan mai karatu na bukata zai iya duba daruruwan girke-girke da muka koyar a baya. Abubuwan hadawa Tafashashshen shinkafa Agada (plantain) Karas Koren w...

 • Yadda ake hada potatoe balls

  Posted Feb 11

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Inda yau zan gabatar da yadda ake hada potatoe balls, in ba'a manta ba a baya munyi bayani akan yadda za ki hada shredded chicken sauce da wadansu miyoyi na zamani. Abubuwan hadawa Potato...

 • Yadda ake hada shredded chicken sauce

  Posted Feb 11

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. Inda yau zan gabatar da yadda ake hada shredded chicken sauce. A baya munyi bayani akan yadda za ki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fried rice da sauran su. Za a iya dubawa....

 • Yadda ake hada potatoe soup

  Posted Feb 11

  Assalamu Alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan gabatar da yadda ake hada potatoe soup. A baya munyi bayani akan yadda zaki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fries rice da sauran su. Abubuwan hadawa Dankali (i...

View All