Makalu

Yadda ake hada meatpie

 • Barkanmu da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau kuma nazo mana da yadda ake hada meatpie baked ko fried.

  Abubuwan hadawa

  1. Nama
  2. Dankali
  3. Carrots
  4. Tarugu
  5. Albasa
  6. Maggi da Seasoning
  7. Fulawa
  8. Butter(1 tblspn)
  9. Baking powder

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki zuba flour ki sa baking powder da butter da dan cube na maggi ki sa ruwa ki hada dough ki buga sosai ya hade. Sai ki rufe ki ajiye.
  2. Ki tafasa naman sai ki daka shi, ki dafa dankali da carrots tare ki hada sai a zuba cikin naman ki sa maggi da gishiri da albasa. Ki juya ki dan barshi na 5 minutes ya dahu.
  3. Ki dauko dough din ki dinga rolling ki fitar da circle sai ki saka filling ki sa bakin fork ki danne. Haka za ki tayi har ki gama. Ki kada kwai daya sai ki yi egg wash na saman. Za ki iya baking ko ki soya duk yadda ki ke so. A ci lafiya

  Za a iya dubaYadda ake hada potatoe balls da yadda ake hada juice na abarba da kankana da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Yadda ake hada ladoos

  Posted Mar 12

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada Laddoos. Abubuwan hadawa Condensed milk Powered milk ko wane irin Biscuit plain desiccated coconut Nutella Sprinkles Yadda ake hadawa ...

 • Yadda ake hada spicy pancakes and potato fillings

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum, barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada spicy pancake and potatoe fillings. Abubuwan hadawa Filawa Tarugu Albasa Dankali (Irish) Maggi Seasoning Kwai Man gyada Baking powder Yadda a...

 • Yadda ake hada sweet pancakes

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada sweet pancake. Abubuwan hadawa Filawa Sugar Baking powder Kwai Chocolates Nutella Dark chocolates Maltesers Smarties Yadda ake hadawa Far...

 • Yadda ake hada milky nut pap

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada milky nut pap. Abubuwan hadawa Farar shinkafa ta tuwo Gyada Madara Dabino Sugar Yadda ake hadawa Farko za ki jika farar shinkafa sai ki gyara ...

 • Yadda ake peppered soup na kaza

  Posted Mar 11

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan koya mana yadda ake hada peppered soup na kaza. Abubuwan hadawa Kazan Hausa Tarugu da tattasai Albasa  Lawashi Curry Maggi da seasoning Tafarnuwa Tandoori Chicken sp...

View All