Makalu

Yadda ake hada grilled gizzard

 • Assalamu Alaikum barka da sake saduwa a fannin girke girkenmu na Bakandamiya. A yau zan gabatar da yadda ake hada gizzard mix. A baya munyi bayani akan yadda za ki hada vegetable rice, da cabbage sauce, da tumeric fried rice, crispy samosas da sauran su.

  Abubuwan hadawa

  1. Gizzard (bulukunji/kundu)
  2. Tarugu
  3. Seasoning da spices
  4. Albasa
  5. Garlic
  6. Mai
  7. Kwakwamba (cucumber)
  8. Tomatoes

  Yadda ake hadawa

  1. Farko za ki wanke gizzard dinki sosai sai ki zuba shi cikin foil paper a dora kan tray na oven asa albasa
  2. Ki dan gasa on Low heat. Sai ki fito da tray ki zuba seasoning garlic ki tarfa oil ki sa tarugun ki ba sosai ba ki sake mayarwa.
  3. Idan ya gasu y rage qarfi sai ki saka Tomatoes da Cucumber a juya a sauke aci.

  Karanta waddannan: Yadda ake hada crispy samosa da yadda ake hada potato magoudas da sauransu.

Comments

Makalu da Dumi-duminsu

 • Nazari kan hukunce-hukuncen ittikafi

  Posted May 25

  Ma'anar ittikafi: Ittikafi shine lizimtar masallaci don bautawa Allah Madaukakin Sarki. Hukuncinsa: Sunnah ne, ba ya wajaba sai ga wanda ya yi bakance akansa. Dalilin haka ya tabbata daga Al-Kur'ani da Hadisai da ijma'in malamai. Dalili daga Al-Kur'ani Allah Ya ...

 • Shar’antattu daga cikin ladubban mai yin azumi

  Posted May 23

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya. Lallai Allah Ya shar'anta wasu ladubba ga ibadar azumi, wanda ya dace mumini ya yi riko da su, saboda ya yi azuminsa cikin cikakkiya...

 • Tasirin fina-finai a kan al’adun Hausawa: Keɓaɓɓen nazari a kan wasu Ɗabi’u na musamman a cikin fina-finan Hausa

  Posted May 22

  Maƙalar da aka Shirya Gabatarwa a Taron Ƙara wa Juna Sani na Ƙasa-da-ƙasa a Kan Gudummuwar Fasaha ga ci Gaba, Wanda Tsangayar Fasaha da Addinin Musulunci, Jami’ar Bayero, Kano ta Shirya, Daga Ranar Laraba 5 ga Watan Oktoba Zuwa Ranar Asabat 8 ga Watan Oktoba, Shek...

 • Abubuwan da suke karya azumi

  Posted May 20

  Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa, da wadanda suka biyo bayansu har zuwa rananr sakamako. A wata makala da ta gabata mun yi bayani akan falalar azumin watan Ramalana inda muka ka...

 • Yadda ake hada tuna muffins

  Posted May 19

  Asaalamu alaikum, barka da saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya a yau. Zamu yi bayanin yadda ake hada tuna cheese muffins ne a yau. Abubuwan hadawa Tuna fish 2 Kwai 2 Gishiri Yaji Grated karas Corn flour Yankakken tattasai Yankakken koren tattasai ...

View All